1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An ci tarar mata saboda tauye hakkin mazan Faransa

December 16, 2020

Ma'aikatar Kula da Harkokin Gwamnati a Faransa ta ci 'tarar' Euro 90,000 ga hukumar gudanarwa ta birnin Paris. Babban laifin da aka samu hukumar da shi shi ne nada mata masu yawa a manyan mukamai fiye da maza.

https://p.dw.com/p/3mmmp
Frankreich Paris Bürgermeisterin Anne Hidalgo nach der Kommunalwahl
Hoto: Imago Images/Le Pictorium/O. Donnars

Ofishin magajin garin Paris da ya yi wannan laifi tun a shekara ta 2018, ya nada mata guda 11 a manyan mukamai sannan ya nada maza guda hudu, abin da ke nufin an yi wa maza danniya ke nan.


Wannan kuma ya saba wa dokar daidaiton jinsi da aka kafa a Faransa a shekara ta 2013 wace ta yi tanadin  cewa daga lokacin kada a sake nada wani jinsi ya haura kaso 60 cikin 100 na manyan mukaman gwamnati. Sai dai da ta ke mayar da martani game da tarar Euro 90,000 da aka ci su, shugabar ofishin magajin garin Paris Anne Hidalgo ta ce matakin ya saba ka'ida kuma abu ne mai matukar hadari.