1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan sassauta radadin dokar ta baci

July 11, 2013

Bayan sanar da shirin tsagaita wuta a tsakanin gwamantin Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram, mahukuntan kasar sun ce ba su da niyyar dakatar da dokar ta bacin da suka kafa makonnin baya.

https://p.dw.com/p/196Ta
Hoto: DW/A. Ubale Musa

Ana dai kallon sabon matakin tsaida wutar a matsayin babban yunkuri a kokarin ganin bayan rikicin da ya tada hankula, sannan kuma ya dora kasar bisa taswirar kasashen dake fama da ta'addanci a cikinsu.

To sai dai kuma gwamantin kasar ta Najeriya tace bata da shirin mika kanta ga borin domin hawa, har sai ta tabbatar da sahihanci tsakanin daukacin masu ruwa da tsaki a cikin rikicin.

Shugaban kwamitin Kabiru Tanimu Turaki yace dokar tabacin za ta cigaba a jihohin, duk da amincewar bangarorin biyu na tsaida wuta, tare da bude shafin tattaunawa a tsakaninsu har sai lokacin da aka tabbatar da ajiye makaman masu fufutakar, dama dawo da zaman lafiya baki dayansa cikin yankunan da abun ya shafa.

To sai dai kuma duk da cewar soja za su cigaba da kasancewa a cikin yankin har sai "baba-ta-gani", daga dukkan alamu mahukuntan kasar ta Najeriya sun fara daukar jerin matakan rage radadin dokar, musamman ma a watan Ramadana mai alfarma inda fadar gwamantin tace a rabawa al'ummar jihohin buhu dubu 390 na abinci iri iri, domin saukaka musu wahalar azumin a cikin sabon yanayin dake zaman ba sabun ba garesu.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten
Yaki da kungiyar Boko Haram a kudu maso gabacin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Dr. Yarima Lawal Ngama dai na zaman karamin ministan kudin tarrayar Najeriya kuma daya daga cikin ministocin da ke jagorantar shirin rabon abincin da gwamnatin ke fatan zai rage radadin dokar.

To sai dai koma wane irin tasiri abincin gwamantin ke iyayi ga rayuwar mutanen jihohin uku dai, ga Abdurrahaman Kocham dake garin Mubi daya kuma daga cikin garuruwan da dokar tai tsamari, ko bayan batu na abincin babban fatansu na zaman sake basu damar magana da yan uwansu da dokar ta katse yanzu haka.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Gwaamnan jihar Borno Kashim Shettima,Hoto: DW

Sannu a hankali dai ana samun rahotannin sake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a daukacin jihohin da a baya ake yiwa kirarin tarkon mutuwa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu