1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance matsalolin Afirka a taron AU

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 2, 2018

Batun hare-haren ta'addanci da wasu kasashen yankin Sahel suka fuskanta a karshen mako da yaduwar yake-yake a kasashen Afirka, ya mamaye taron kolin kungiyar Tarayyar Afrika da ya gudana a kasar Moritaniya.

https://p.dw.com/p/30hPa
Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel
Hoton shugabannin Afirka a wani taron koli da suka yi a baya a birnin Addis AbabaHoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

Taron koli da ke zaman karo na 31 na kungiyar ta Tarayyar Afirka, ya kuma yi nazarin hanyoyin da ya kamata su bi domin rage kaifin matsalar cin hanci da Rashawa. To sai dai kuma irin yadda a karshen mako aka kai harin ta'addanci a shelikwatar rundunar tsaro ta G5 Sahel da ke a birnin Sevare na tsakiyar kasar Mali, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu wasu kimanin 20 da suka hada da sojojin Faransa na rundunar Barkhan suka jikkata, a yayin da wasu sojojin gwamnatin Nijar 10 suka hallaka wasu hudu suka bata a sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan sojojin Nijar a yankin jihar Diffa ya mamaye taron baki daya. Ko wace fassara za a iya yi wa wadannan hare-hare da ake fuskanta a yankin na Sahel duk da tarin rundunonin soja daban-daban na ketare da na kasashen yankin? Nasser Burita ministan harakokin wajen kasar Maroko ya bayar da amsa yana mai cewa:

Mali Angriff auf G5 Sahel Basis in der Stadt Sevare
Sansanin rundunar G5 Sahel a Mali da aka kai wa hariHoto: Getty Images/AFP

A bayyane take cewa reshen kungiyar Alka'ida mafi karfi na nahiyar Afirka, inda yake da mayaka sama da 6000 sannan ga mayakan kungiyar IS kimanin 3000 da suma suka yi kaka gida a Libiya da sauran kasashen yankin bayan da aka fatattake su daga Siriya da Iraki, baya ga mayakan al-Shabab da Boko Haram

Wanne mataki Macron ka iya dauka?

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron wanda kasarsa ke a sahun gaba wajen fafutikar kafar rundunar ta G5 Sahel ya halarci taron kolin na kungiyar ta AU inda daura da taron zai tattauna da shugabannin kasashen kungiyar ta G5 Sahel kan halin da ake ciki a yankin. To ko wani mataki Shugaba Macron zai iya dauka kasancewa wannan ba shi ne karo na farko ba da ake harar da sojojin kasar Faransar a Mali?.Paul Melly na cibiyar Chatham House mai nazarin siyasar duniya da ke London na da wannan ra'ayi:

USA Präsident Macron Besuch
Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Ina ganin ba zai yi mamaki ba, harin da aka kai wa wasu daga cikin sojojin Faransa a yankin Goa  ko Kidal na kasar ta Mali abu ne da ya zama ruwan  dare, gwamnatin Faransa ta kwana da sanin irin wadannan hare-hare za su cigaba, a yanzu tambayar ita ce ko Faransa za ta iya taimakon kasashen G5 Sahel ta hanyar kara karfin sojojin da ke aikin tsaro a wannan yanki? Wannan shi ne babban kalubalen da ke gaban Faransa.
 

Ko baya ga batun yankin Sahel taron kolin kungiyar ta AU ya tattauna batun yake-yaken da ake fuskanta a wasu kasashen nahiyar kamar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Somaliya da Sudan ta Kudu da suka ki ci suka ki cinyewa duk da jerin kudurori daban-daban da shugabannin nahiyar ke dauka a jerin tarukan da suke gudanarwa. Sai dai Pierre Bouyoyya wakilin kungiyar AU a Mali da yankin Sahel na ganin zaman lafiya batu ne da ke bukatar lokaci. Abin jira a gani dai shi ne tasirin da shawarwarin da taron na birnin Nouakchott ya cimma za su yi wajen shawo kan jerin matsalolin tsaro da kusan illahirin kasashen nahiyar Afirkan ke fuskanta.