1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin yin fida ga mata maimakon nakuda

Zulaiha Abubakar AMA
June 17, 2019

A cikin shirin na wannan makon za a ji dalilan da ke sanya wasu matan da suka dauki ciki ke zabar matakin yi musu fida a yayin haihuwa maimakon su yi nakuda su haihu da kansu a wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3KaBi

Sannu a hankali bakuwar al'adar haihuwa ta hanyar fida maimakon nakuda na fara karade sassa dabam-dabam na kasashen Afirka ciki kuwa harda arewacin Najgeriya. A baya dai akan yiwa mace fida ne idan har haihuwa tazo da tangarda ko kuma idan likitoci sun gano ba zata iya haihuwa da kan ta ba, to amma  sai ga shi daga baya 'yan kwari da masu hannu da shuni su zabi biyan kudade don yi masu fida tare da cire jarirai