1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HdM: Manhajar sayen tikitin jirgin kasa

January 27, 2021

Wani matashin dan jarida kwararre a harkar kimiyya da fasaha da ya saba zuwa tashar jirgin kasa ta Kaduna zuwa Abuja dauko rahotanni, ya kirkiro wanita mahajar sayan tikitin jirgin kasan.

https://p.dw.com/p/3oUIv
Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Fasinjoji na shan wuya wajen sayen tikitin jrgin kasan da ke zirga-zirga daga Kaduna zuwa AbujaHoto: DW/U. Musa

A kokarinsa na warware matsalar cincirindo da wahalhalun da dubban matafiya a tashar jirgin kasa ta Kaduna zuwa Abuja fadar gwamnatin Najeriya ke fuskanta ne dai, matashin mai suna bdulganiyu Alabi da kuma ya kasance dan jarida ya kirkiro manhajar. Da ma dai ya saba adauko rahotanni daga tashar jirgin kasan ta Kaduna, inda ya kasance ganau ba jiyau ba dangane da wahalhalun da matafiyan ke sha, inda kuma ya saukaka musu ta hanyar wannan manhaja da za ta ba su damar yin amfani da wayoyin hannunsu su sayi tikitin ba tare da shan wahala ba.

Matashin ya ce wannan manhajar na da matukar muhimmanci, musanman ma dai wajan taimakawa matafiyan rage irin wahalhalun da suke fama da su kama daga bin dogon layi da shan ranazuwa ga rage wasu kalubalen da suke fuskanta yayin da suke shirin zuwa tashar jirgin kasan domin tafiya zuwa Abuja. Abdulganiyu ya kara da cewa bayan wani horo da ya je na gajeren lokaci da wani kamfanin na'urorin sadarwa na zamani ne dai, aka umurci kowa ya kirkiro wani abu da zai iya,wanda zai taimaka wajen warware matsalolin da al'umma ke fama da su, hakan ce ta sanya shi mayar da hankali a kan kirkiro wannan manhajar domi taimaka wa hukumomi da al'umma matsalolin da ke janyo koma baya a wannan bangaren.

Matashin ya ce, ya cimma tarin nasarori da wannan na'urar da ya kirkira, duk kuwa da ce akwai manyan kalubalen da ya fuskanta, musamman yayin da yake karbar horon kirkirar na'urar.