1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Karfafa samar da matatun man fetur a Najeriya

November 24, 2020

Gina matakan kawo karshen shigo da man fetur domin amfani na 'yan kasa, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da matatar man fetur ta farko ta masu kasuwa da za su taka rawa a cikin harka ta kasuwancin man cikin kasar.

https://p.dw.com/p/3lliV
Erdölindustrie in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/Göttert

Duk da cewar dai mutnanen kasar na bukatar man da ya kai lita miliya 50 da doriya a kusan kullum, kaso dari cikin dari dai na fitowa ne daga kasashen waje. Najeriya dai tana zaman kasa daya tilo a cikin jerin manya na kasashen OPEC ta masu arzikin man fetur din da ke dogaro da kasashe na waje wajem bukatar ta makamashin man fetur mai tasiri. To sai dai kuma gwamnatin kasar na neman sauyawa tare da wani sabon shirin samar da kananan matatu da kasar ke fatar za su maye gurbin manyan da suka lamushe dubban miliyoyi na daloli suka kuma kasa biyan bukatar 'yan kasar.  Najeriya: Adawa da karin farashi

Najeriya dai ta ba da akalla izinin gina matatun 13 shekaru biyu baya a kan hanyar wadatar da kasar da hajjar man fetur ya zuwa shekaru uku masu zuwa. Abuja ta kaddamar da matatar farko da aka tsara za ta tace ganga 5,000 na danyen man kullum.  Najeriya: Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2020

Erdöllraffinerie in Nigeria
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Shugaban kasar Muhammadu Buhari dai ya ce kasar tana kan hanyar cika burin wadata kai da bukatar makamashin man fetur a karkashin shiri na gwamnatin da ya faru a shekaru biyu baya.  

Sabuwar matatar dai na zaman sabon fata ga kasar na mai da kasu alkali a cikin harkar tace man da kafin yanzu ke zaman hurumin yan mulki na kasar. Kuma a fadar Mallam Garba Shehu dake zaman kakaki na gwamnatin, Abuja na fatan iya kai wa ga wadatar da kanta da harkar mai a cikin kankanen lokaci a karkashin sabon tsarin. Najeriya dai na yi wa harkar tace danyen man kallon tsaf a cikin fatan kai karshen rikicin man fetur da ko bayan asarar kudin shiga ga kasar, ke iya komawa damar samun aiki a tsakanin miliyoyin 'yan kasar. Kuma a fadar Mele Kyari da ke zaman shugaba na kamfanin mai na kasar NNPC, kasar tana shirin gyara manyan matatun guda hudu cikin neman rage dogaro da kasashen waje ga bukatar hajjar.  Farashin man fetur ya tashi