1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar banbancin launin fata a Jamus

March 21, 2006

Matsalar launin fata ta dauki wani sabon salo na kyamar musulmi a Jamus

https://p.dw.com/p/Bu14

Wani abin da ake gani a rayuwa ta yau da kullum a nan kasar, in ji Klaue-Machangu shi ne idan mutum ya shiga motar safa ya nemi kujera ya zauna da zarar Bajamushe ya shigo zai nemi guri ne can nesa da bakar fata ko da kuwa motar ta cika ne makil, in ma har zarafi ya kama tilas ya zauna kusa da bakar fata to zai zauna ne ta yadda ba zai shafe shi ba.

Ita dai Eva Klaue-Machangu ‘yar usulin kasar Tanzaniya ce dake rike da takardar fasfo din Jamus kuma tayi sama da shekaru 30 tana zaune a kasar tare da mijinta Bajamushe. Amma duk da haka tana fuskantar banbancin launin fata a rayuwa ta yau da kullum. Ire-iren wannan wariya sakamakon banbancin launin fata abu ne dake illa ga rayuwar mutanen da lamarin ya shafa. Akwai misalai da yawa game da haka in ji Stefen Keßler wakilin kungiyar Amnesty akan yaki da wariyar jinsi a Jamus:

“Sau tari masu tsaron kofa kan hana mutum shiga gidajen rawa saboda launin fatarsa, misali idan baturke ne sai su ce wai akwai turkawa da yawa a ciki. Ko kuma mutum ne ke neman gida, sai mai gidan ya ce da shi ba ya ba wa bakar fata hayar gidansa.”

Ire-iren wadannan kalamai suna masu tunasarwa ne da farfagandar ‘yan Nazinhitler a kasar ta Jamus. Sau tari abubuwa ne da aka gada tun daga kakannin kaka, kamar dai wani wasa da ‘yan yara kan yi a karkashin taken:Wa ke tsoron bakar fata?

To sai dai kuma wani da ake kira Ralf-Eric Posselt mai hadin kai da makarantu da kananan hukumomi domin yaki da matsalar banbancin launin fata ya fi dora alhakin sabon yanayi na wariyar da aka shiga akan jami’an siyasa ne da kafofin yada labarai, wadanda a yanzu haka suke saka ayar tambaya a game da zama na cude-ni-in-cude-ka tsakanin jinsunan mutane daban-daban, musamman ma masu banbance-banbance na addinin kamar musulmi. Babban misali a nan shi ne goyan bayan da jam’iyyar CDU ta nema daga jama’a domin adawa da karbar kasar Turkiyya a Kungiyar Tarayyar Turai, ko kuma jarrabawar da ake wa Musulmin dake neman zama ‘yan kasa a Jamus a wasu jihohi na kasar yanzu haka. Kyamar baki da wariyar launin fatar ya fi tsamari ne a gabacin kasar, inda ake fama da dimbim marasa aikin yi. A wannan yanki an yi shekara da shekaru masu zazzafan ra’ayin wariya na kai farmaki kan baki. Amma ita ainifin akidar ta wariyar launin fatar gama gari ce a zukatan illahirin Jamusawa.