Matsalar cin zarafin mata a Amirka ta karu
May 1, 2014Talla
Wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta Amirka wato Pentagon ta fitar, ya nuna yadda alkaluman irin kararakki da ake samu na cin zarafin mata a wuraren aiki ke karuwa. A cewar Pentagon, duk da irin kokarin da hukumomi ke yi na magance lamarin, amma kuma sai karuwa yake yi. Rahoton yace a shekaru biyu da suka gabata, an samu karakin cin zarafin mata kimanin 3,374. Amma kuma a bara alkaluman sun karu da kashi 13, abinda kuma ya sa yanzu yawan matsalar cin zarafin ta kai kashi 50 cikin dari. Lamarin da kuma hukumomi suka ce na tada hankali ne.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Naisru Awal