1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar fashin teku a kasashen Afirka

December 28, 2012

Yayin da fashin jiragen ruwa ya ragu a gabar tekun Somaliya, matsalar sai habaka ta ke yi a gabar tekun Guinea dake a yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/17AJ8

A wannan makon mafi yawan jaridun na Jamus sun mayar da hankali a kan fashin jiragen ruwa a gabar tekun Guinea wato Gulf of Guinea. A labarin da ta buga kan wannan batu jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa.

"Duk mai kokarin kimanta hatsarin da ake fama da shi kwanan nan a gabar ruwayen Afirka, to zai ga abubuwa guda biyu. Na farko fashi a ruwa a tekun Indiya inda 'yan fashin ruwa na Somaliya suka kwashe shekaru suna aikata ta'asa, ya ragu, na biyu shi ne munin da wannan aika-aika ta yi a daya bangaren na Afirka wato gabar tekun Guinea dake yammacin nahiyar." Jaridar ta ce "tun ba yau ba 'yan bindiga a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya ke kai wa kamfanonin mai hare hare. Amma yanzu ana ganin yadda wannan aika-aika ta tashi daga doron kasa zuwa kan ruwa. 'Yan fashin tekun ba a gabar ruwayen Najeriya kadai suke wannan ta'asa ba, sun kuma addabi kasashen Kamaru, Equitorial Guinea, Togo, Benin da kuma tsibirin Sao Tome da Principe. Yanzu haka yankin gabar tekun yammacin Afirka ta zama daya daga cikin yankunan mafiya hatsari ga sufurin jiragen ruwa a duniya, sannan kasashen da abin ya shafa sun kasa yin wani katabus don tinkarar wannan matsala."

karuwar fashin ruwa a yammacin Afirka

Ita ma jaridar Berliner Zeitung rahoto ta buga a kan fashin tekun tana mai cewa: A yammacin Afirka fashin jiragen ruwa na habaka, inda ya zama wata kafar samun kudi, yayin da a gabar tekun Somaliya fashin ya yi sauki.

EU-Einheit Somalia Piraten Angriff
Hoto: picture-alliance/dpa

"A ranar 23 ga watan Disamba 'yan fashin tekun suka farma wani jirgin ruwan kasar Italiya a gabar tekun jihar Bayelsa ta Najeriya. Babu jami'an tsaro a cikin jirgin, kuma bisa ga dukkan alamu an tsegunta wa 'yan fashin." Jaridar ta ce fashin jirgin da kuma garkuwa da ma'aikatansa ya kusan zama ruwan dare a wannan yanki na gabar tekun Guinea, inda a bara aka yi fashin jiragen ruwa 64, abin da masana tattalin arziki suka yi kiyasin cewa na janyo asarar kudi dala miliyan dubu biyu a shekara."

Rashin raba daidai a Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu na fama da rashin daidaito tsakanin al'umma shugaba jacob Zuma ya kasa shawo kan matsalar, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta na mai mayar da hankali da koma-bayan tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu.

"Masu saka jari na fargabar habaka harkokinsu a wata kasa da babu tabbas, amma babban taron jam'iyar ANC, inda aka sake zaban shugaba Jacob Zuma da ya jagoranci jam'iyar a zaben kasar dake tafe, ya tabbatar wa kamfanoni cewa gwamnati ba za ta mayar da su mallakinta ba. Da farko dai masu ra'ayin sauyi na reshen matasan jam'iyar ANC sun yi kira da gwamnati ta dora hannu kan kamfanoni masu zaman kansu. Sai dai jaridar ta ce babu wani abin da zai sauya ga kusan rabin 'yan Afirka ta Kudu dake rayuwa cikin matsanacin talauci. Kusan iyalai miliyan biyu ba su da albashin kansu, yayin da matsalar cin hanci da rashawa ta yi katutu a muhimman ma'aikatun gwamnati kamar fannin ilimi da kiwon lafiya. Sai dai ba karancin kudi kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ke fama da shi ba, matsalar shi ne rashin raba daidai tsakanin 'yan kasar.

Seychellen Piraten Festnahme
Hoto: picture alliance / dpa

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe