1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makarantu a wasu yankunan Kamaru na cikin matsala

Usman Shehu Usman
November 11, 2018

Bayan sace 'yan makarantar da aka yi satin da ya gabata cocin Presbyterian ya rufe daukacin makarantunsu da ke yankin Ingilishi na kasar Kamaru sai yadda hali ya yi.

https://p.dw.com/p/382y1
Kamerun | Erzbischof Cornelius Fontem Esua
Hoto: DW/A. Kriesch

Ko da a jiya Asabar wasu 'yan bindiga uku sun shiga makarantar Progressive Comprehensive High School (Pchs Mankon) da ke a Bamenda babban birnin yankin arewa masu yammacin Kamaru. A cewar Baba Abdullahi, wakilin DW Hausa a Bamenda, 'yan bindigan da suka shiga makarantar sun gargadi malaman makarantar da su rufe makarantar ko su gamu da fushin mayakan. Baba Abdullahi ya bayyana cewar nan take bayan samun labarin gwamnatin Kamaru ta tura karin jami'an tsaro don gadin makarantar da kuma karfafa gwiwa ga malamai da dalibai.