1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar shara a lokacin aikin hajji

October 16, 2013

Alhazai da suka fito daga kasashen Afirka na zubar da abinci a wuraren da suke zama a Minna ba tare da hukumomin saudiya sun kwashe ba, inda ya ke barazana ga lafiyansu.

https://p.dw.com/p/1A19a
Hoto: DW/A. Abubakar

Alhazai musamman daga kasashen Afirkca na zama a cikin shara da kazanta na abincin da suke ci, suke kuma zubarwa a zaman ibada na Minna da suke kan yi don jifan shedan. Alhali irin hakan ya taba haifar da cutar kwalara a 'yan shekarun da suka wuce. Ko su ma alhazan Najeriya suna ma'amala ne da wannan kazanta na shara saboda hukumomin Saudiyya sun kasa shareta, duk da sanin da suka yi cewa tara yawan mutane da dama a wuri daya kan kawo yawan shara.

Korafin alhazai ga hukumomi
Wani Alhaji dan asalin Najeriya mai suna Umar Maccido wani ya ce gaskiya harkar tsabta a nan Muna a na bukatar karin kulawa, saboda " bara na zo wannana wurin, na ga irin yadda abubuwan suke, kuma kusan duk abu gudane. Saboda tsabta abu ne mai muhimmaci wanda in babu ita, sai abincin da za ka ji ma ya jawo maka kwalara ko wani ciwo daban.

Islam Hadsch Zeremonie Saudi-Arabien Mekka
Matsalar shara bata yi kamari a Makka baHoto: Reuters

Shi kuwa Sagir Gambo da ya fito daga Kano kira ya yi da a dauki matakan da suka wajaba don ganin cewa an kwashe sharar cikin hanzari. Ya na daga cikin wadannan sharar da hana wa sayan abinci a wata runfar sayar da abinci. Ya ce " Ya kama tahukumar Saudi Arabiya ko kuma ta Najeriya su san matakin da za a dauka, domin kwasheta. Gaskiya abun ya na bukatar a duba “.

Illolin da ke tattare da tare shara
Jamian lafiya na Najeriya sun dukufa wajen wayar da kan alhazansu a kakafen yada labarai na jihohinsu da suka kafa a nan Minna kan illolin zama da cin abunci wuri daya da kazanta. Dr Bello Ahmed ya ce lamarin kan iya haifar da cututtuka irin su ciwon ciki da gudawa matikar dai ba a dauki matakai ba. Ya ce " Idan aka bari tarin sharar nan yay i yawa, akwai matsalolin da yake iya jawowa masu dama: Na daya dai akwai yiyuwar samun cututtuka kamar su yawan ciwon ciki, wanda daga nan ya na iya wucewa zuwa amai da gudanawa. "

DW ta tuntubi wasu shugabannin hukumomin alhazai na jihohin Najeriya dake Minna a kan matakan da suka dauka don kaucewa alhazansu kamuwa da cututtuka a zaman da suke yi na Minna. Alhaji Muktar Maigona shugaban alhazai na jihar Sokoto ya ce ” hukumar jin dadin alhazai na jihar Sokoto ta dauki matakai a kan matsalar shara a Minna . Shi ya sa ta kafa kwamitin kula da tsabta."

Haddsch Pilgerfahrt
Alhazan Afirka ne suka fi zubar da shara a saudiyaHoto: AFP/Getty Images

Matakan da ake shirin dauka
Wani jami'i na hukumar alhazai ta Najeriya dake nan Minna da baya so na ambaci sunansa, ya sheda wa DW cewa sun kai koken su ga hukumomin na Saudi Arabiya. Kowani lokaci daga yau za a soma kwashe jibgin shara da ya mamaye dukkan hemomin alhazan Najeriya da ke Minna don gudun bullar cututtuka na kwalara a wuraren.


Mawallafi Aminu Abdullahi Abubakar daga Minna
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe