1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa na barazana ga duniya

Usman Shehu Usman
April 3, 2019

Bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashe Takswas a duniya da bala'in yunwa ke yin barazana rayuwansu inda binciken ya gano mutane kimanin miliyan 113 ke fiskantar barazana bisa rashin abinci a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3GCBD
Moatize, Tete Provinz, Mosambik
Hoto: DW/Amós Zacarias

Wata kungiya kasa da kasa ta fidda rahoto kan rashin abinci mai gina jiki a duniya, rahoton wanda hadin gwiwar kungiyoyin duniya kamar su FAO da WFP da Tarayyar Turai da sauransu suka fitar, ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 113 cikin kasashe 53 ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki. Kasashe Takwas da lamarin ya fi tsanani suna ne, Najeriya, Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, Sudan ta Kudu, Habasha, Siriya, Sudan da kuma kasar Yamen. Kuna iya sauraron dalilan da suka sa kasa kamar Najeriya ta kasance a sahun kasashe takwas da ke fama da yaki kamar Yamen, Siriya da Sudan ta Kudu, a hirar da DW Hausa ta yi da Dr .Mairo Mandara, babbar jami'a a cibiyar kula da yara da ke Birtaniya, kana wace ta kafa kungiyar lura da yara mata a Najeriya.