1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsanancin karancin mai a Najeriya

Ibrahima YakubuMay 25, 2015

Kampanoni da kafofin watsa labarai da bankuna sun fara tsayar da aikace-aikacensu sabili da matsalar karancin man petur da ya addabi kasar.

https://p.dw.com/p/1FWDv
Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/E. Arewa


A yanzu dai yunkurin rufewar wasu kafafen sadarwa da kampanoni da bankuna da ma'aikatu da masana'antu a Najeriya saboda matsanancin matsalar karancin man fetur da ke neman durkusar da alamurran rayuwar talakawan kasa.

Tun kusan kwanaki 3 da suka gabata ne wasu kafafen watsa labarai a cikin kasar suka fara dakatar da ayyukansu saboda karancin man fetur dake addabar su, lamarin da ke neman gurgunta harkokin watsa labarai da shiga kafafen sadarwa na zamani a cewar Mr john Adoko wani kwararre a bangaren harkokin sadarwa.

A yanzu haka dai Najeriya ta kasance akan gaba,fiye da sauran kasashen Duniya wajan safarar kananan Injinan da ake amfani da su a gidajen wajan samar da makamashi na wutar lantarki, lamarin da ke nuni da cewa shakar hayakin wadannan janaretoci na da munmunar illa ga rayuwar bani adama.

Ya zuwa wannan lokaci dai wannan matsala ta karancin man fetur ta Tursasa Miliyoyin jama'a da kananan yara shiga tattaki wajan zuwa wuraren harkokin su na yau da kullu,lamarin dake bukatar sabuwar gwamnati ta cetosu daga cikin matsananciyar rayuwar da suka fada ciki.