1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsaya kan kafa gwamnatin hadin guywa a Jamus

November 27, 2013

Jam'iyyar CDU ta Merkel da kuma Takwarata SPD mai adawa sun cimma matsaya a kan kafa gwamnatin hadun guywa. Sai dai kuma yarjejeniyar ba za ta fara aiki ba, sai bayan magoya bayan SPD sun kada kuri'ar raba gardama..

https://p.dw.com/p/1APTT
(L-R) German Chancellor Angela Merkel, Sigmar Gabriel, leader of Germany's social democratic SPD party, CSU chairman and Bavarian State Premier Horst Seehofer walk through a corridor at Willy Brand-Haus, SPD's headquarters, for talks between German Chancellor's conservative CDU/CSU union and the social democratic SPD in the aim of forming a coalition government in Berlin on October 30, 2013. AFP PHOTO /JOHN MACDOUGALL (Photo credit should read JOHN MACDOUGALL/AFP/Getty Images)
Hoto: JOHN MACDOUGALL/AFP/Getty Images

Sa'o'i 18 jam'iyyun CDU/CSU da kuma SPD suka shafe shuna shawarwari tsakaninsu kafin su amince su jera tare cikin shekaru hudu masu zuwa. Wannan dai ba shi ne karo farko cikin tarihin Jamus ba, da bangarorin biyu suka hada guywa domin tafiyar da harkokin mulki. Ko da a wa'adinta na farko, sai da Angela Merkel ta CDU ta jera da Jam'iyyar ta SPD. Sai dai kuma a wannan karon, gwamnati ba za ta fara aiki ba, sai idan magoya bayan jam'iyyar SPD sun kada kuri'ar raba gardama kan dacewar jerawa da Merkel tsakanin ranakun shida zuwa 12 ga wata Disemba.

Sai dai kuma Klaus Shubert, malamin kimiyar siyasa a jami'ar Münster ya ce babu tabbas game da samakon kuri'ar saboda banbance-banbance da ke tsakanin SPD da kuma CDU/CSU. ya ce " Shugaban SPD na karshen da ya samu karfin fada a ji shi ne Willy Brandt, wanda ya yi amfani da gogewarsa ta siyasa wajen cimma burinsa. Amma shi ma na yanzu wato Siegmer Gabriel, ya dauki tsawon lokaci wajen ganin cewa kwalliyarsa ta mayar da kudin sabulu,ta yadda magoya bayan jam'iyyar za su yi na'am da matakin da uwar jam'iyya ta dauka"

Secretary general of the Christian Social Union (CSU) Alexander Dobrindt (R) and Christian Democratic Union (CDU) party secretary general Hermann Groehe gives a statement to the media after coalition talks with the Social Democratic Party (SPD) at the SPD headquarters in Berlin, November 27, 2013. German Chancellor Angela Merkel's conservatives and the centre-left Social Democrats (SPD) made a breakthrough early on Wednesday in talks about forming a "grand coalition" government, two top conservative politicians said on their Twitter accounts. REUTERS/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS)
Jam'iyyun CDU da SPD sun hada guywa wajen gudanar da mulkiHoto: Reuters

Manufon da sabuwar gwamnati za ta sa a gaba

Ministoci 15 sabuwar gwamnatin ta Jamus za ta kunsa: tara daga cikinsu za su fito ne daga bangaren masu ra'ayin rikau wato CDU da CSU, yayin da jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gurguzu za ta tashi da kujerun ministoci shida.

Daga cikin manufofin da gwamnatin hadin guyawar za ta sa a gaba, har da kayyade Euro 8,50 a matsayin mafi karancin al'bashi da kowani ma'aikaci ya kamata ya samu a kowani awa. Da ma dai Jam'iyyar SPD da ta zo ta biyu a zaben watan Satumba, ta nace kai da fata sai a amince da mafi karancin albashi matikar ana so ta shiga cikin gwamnatin hadin guywa. Sai dai bangaren Merkel na nunawa cewa zai iya jawo nakasu ga tattalin arzikin wannan kasa, a inda zai haifar da asarar guraben aiki.

Wani muhimmin batu da jam'iyyar SPD ta nace a yi la'akari da shi a wa'adin mulki na gaba, shi ne inganta tsarin pensho na ma'aikatan da albashinsu bai taka kara ya karya ba. Wannan ya na nufin cewa za a bai wa wadanda suka shafe shekaru 45 suna aiki damar yin ritaya a shekara 63 maimakon shekaru 67 kamar yake yanzu haka.

Yawan kudi da gwamnatin Jamus za ta kashe

Aiwatar da wadannan manufofin da jam'iyyun CDU/CSU da kuma SPD suka sa a gaba, ta na bukatar kudi kimanin miliyan dubu 23 na Euro cikin shekaru hudu masu zuwa. Sai dai kuma Gustav Horn, darektan cibiyar tattatalin arziki ta IMK da ke Düsseldorf ya ce wadannan kudade ba za cire wa Jamus kitse a wuta ba. Dalili kuwa shi ne "Muna da wata babbar matsala a Jamus, wacce ba wata ba ce illa lalacewar hanyoyi. Ana ta shigar da kararraki game da wannan batu. Amma kuma ba abin da aka yi illa ware Miliyan dubu 23 na Euro. Wannan kashi daya ne bisa hudu na bunkasar tattalin arzikin Jamus. Za a iya cewa ba za su kai labari ba."

German Social Democratic Party (SPD) General Secretary Andrea Nahles talks to the press after coalition talks with the Christian Democratic Union (CDU) on November 27, 2013 in Berlin. German Chancellor Angela Merkel's conservatives and the centre-left Social Democrats (SPD) made a breakthrough early on Wednesday in talks about forming a "grand coalition" government. AFP PHOTO / JOHANNES EISELE (Photo credit should read JOHANNES EISELE/AFP/Getty Images)
Ranar 27 ga Nov 2013 za ta shiga cikin tarihin CDU da SPDHoto: JOHANNES EISELE/AFP/Getty Images

Passport biyu ga 'yayan 'yan ci-rina a Jamus

Sassa biyu sun yi alkawarin cewa ba za su karin ko da kwabo ba a matsayin haraji. Sannan kuma za su ci-gaba da sauke gammo bashin da ke kan Tarayyar ta Jamus. Hakazalika jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gurguzu ta nace kai da fata sai da aka amincewa cewa 'yayan baki da ake haifa a Jamus sun rike passport biyu wato daya na Jamus da kuma daya na kasarsu ta asali.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu