1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwa kan bacewar Khashoggi a Istanbul

Mahmud Yaya Azare
October 10, 2018

Kawo yanzu an kasa gano inda dan jarida nan dan kasar Saudiyya Jamal Khashoggi yake, mako guda bayan shigarsa karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/36IRT
Türkei Sicherheitspersonal im Konsulat von Saudi Arabien in Istanbul
Jami'an tsaron Turkiyya sun shiga karamin ofishinn jakadancin Saudiyya a IstanbulHoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiyyaa suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyya  Khashoggi mai sukar gwamnati, na nuni da cewa, an kasheshi ne a cikin karamin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya da ke Istanbul kana aka fita da gawarsa aka jefar da ita. Sai dai Saudiyya ta musanta cewa tana da masaniya kan makomarsa, amma ta amsa cewa ya ziyarci ofishin nata a ranar Talata domin karbar wasu takardu, kuma ya fita bayan wani lokaci, kodayake ta kasa tabbatar da yadda ya fita, bayan da ta ce na'urori nadar hotuna da ke ofishin basa aiki, sannan kuma ta bada hutu haka kwatsam ga masu gadi 'yan kasar Turkiya a ranar da wannan lamari ya auku.
 

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya kalubalanci Saudiyya da ta nuna hoton da ke nuni da ya fita daga ofishin, shi ke nan ta wanke kanta inda ya ke cewa:  “Ku da kanku kun tabbatar ya shiga cikin ofishin jakadancinku. Na'urar kan tituna ta nuna hotonsa ya na shiga. Ku kawo mana hotunan yadda ya fice don mu san yadda zamu nemi shi.”

Deutschland Türkischer Präsident Erdogan in Köln
Shugaban Turkiyya Erdogan ya kalubalenci Saudiyya kan bacewar KhashoggiHoto: Reuters/W. Rattay

Shugaban Amurka Donald Trump, ya nuna takaicinsa game da labarin bacewar Kashoggin inda cikin wani jawabi da ya yi yake cewa: “Na damu akan wannan batun da ko kadan bai da dadin ji. Ban ji dadin aukuwarsa ba.”

To sai dai mambobin majalisar dattawan Amurkan sun yi barazanar daukar matakan ladaftarwa idan har ta tabbata Saudiyya ta yi wa dan jaridar kisan gilla: “Idan da gaske Saudiya ta yi kisan gilla ga wannan dan jaridar, to dole ta dandana kudarta. Kuma lalle ya wajaba Amurka ta yi mata tofin Allah tsine.”

Türkei Konsulat von Saudi Arabien in Istanbul
Karamin ofishin jakadancin Saudiyya a birnin IstanbulHoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

Babban jami'in kare hakkokin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya David Kaye, da babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini, da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, duk sun bukaci gwamnatin Saudiyya ta bayar da damar gudanar da bincike domin yaye duhu dangane da makomar Khashoggin.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai Jamal Khashoggi ya tafi karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul da nufin neman wasu takardu a shirye-shiryen da yake yi na auren wata 'yar kasar Turkiyya, to sai dai tun lokacin ba a sake jin duriyarsa ba. Jami'an tsaron Turkiyya da kuma budurwarsa sun ce lalle tun da ya shiga ofishin jakadancin bai fita ba, alhali su kuma jami'an Saudiyyan sun ce ya bar ofishin bayan ya sami abin da ya kai shi.