1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Iran da laifin tallafawa 'yan ta'adda

Ramatu Garba Baba
February 21, 2020

Kungiyar da ke bin diddigin kungiyoyi na masu tayar da kayar baya da hanyoyin da suke samun kudadden shiga, ta tsaurara takunkumi kan kasar Iran tare da sanya wasu bakwai a jerin kasashen da ke tallafawa ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3Y9tB
Frankreich l Financial Action Task Force (FATF) Medienkonferenz - Xiangmin Liu
Hoto: Reuters/C. Platiau

Kungiyar da ke bin diddigin ayyukan 'yan ta'adda da hanyoyin da suke samun kudadden da suke gudanar da ayyukansu, ta karfafa bincike inda ta tsaurara takunkumi kan kasar Iran a yayin da ta kara sanya kasashe bakwai a jerin kasashen duniya da 'yan kasar ko kungiyoyi ke tallafawa ayyukan ta'addanci da kudi ba tare da gwamnati ta ce uffan ba.

Financial Action Task Force ko FATF a takaice, ta dauki mataki kan Iran ne bisa gazawar da ta ce gwamnatin kasar ta nuna a kin hukunta kungiyoyi ko wasu 'yan kasar da aka samu da laifin tallafawa ayyukan ta'addanci. Iran dai ta mayar da martani bayan wannan sanarwar inda ta danganta sanarwar da bita da kullin siyasa a sakamakon matsi daga Amurka da Isra'ila da kuma Saudiyya.

Sauran kasashen da aka sanya a bakin littafin bisa zarginsu da zura ido a yayin da masu bai wa 'yan ta'adda goyon baya ke cin karensu ba babbaka, sun hada da Jamaica da Albaniya da Barbados da Mauritius da Myanmar da Nicaragua da kuma Yuganda, an shawarcesu da su dauki matakin gyara ko kuma su fuskanci karin matakan ladabtarwa daga Kungiyar.