1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta yi mummunan martani a kan Rasha

Zainab Mohammed Abubakar MAB
February 24, 2022

Kwamitin sulhun MDD ya yi kira ga shugaba Vladimir Putin da ya janye sojojinsa daga Ukraine, a yunkurin karshe na kare barkewar yaki a rikicin Moscow da Kiev.

https://p.dw.com/p/47VXD
Ukraine | Ukrainische Panzer in Mariupol
Tankunan yaki na sojojin UkraineHoto: Carlos Barria/REUTERS

Bayan taron gaggawar da wakilan kwamitin sulhu 15 suka gudanar, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce wannan ya kasance lokaci mafi muni da bacin rai, a shekarunsa biyar kan wannan mukami.

Ya ce "Idan har da gaske ne ana shirin kai mamaye, ina ada abu guda kawai da zan fada daga zuciyata: Don Allah shugaba Putun ka tsayar da sojojinka daga kai somame Ukraine. Ka bai wa shirin zaman lafiya dama. Mutane da yawa sun rasa rayukansu a baya"

A hukumance dai shugaba Vladimir Putin ya bada umurnin mamayen yankunan Donetsk da Luhansk da ke yankin gabashin Ukraine, a wani jawabin da yayi ta gidan talabijin na kasa da safiyar wannan Alhamis.

Paris Normandie Treffen | Putin Zelenskyy
Shugaba Putin na Rasha da Zelensky na UkraineHoto: Mikhail Metzel/TASS/dpa/picture alliance

Ya ce, ya zartar da gudanar da wannan mamaya ta musamman na sojoji a wadannan yankuna, da nufin kare rayukan mutane da suka tsinci kansu cikin ukuba da kisan kare dangi na tsawon shekaru takwas.

Matakin na shugaban Rasha dai ya biyo bayan takardar rokon agaji daga shugabannin yankunan biyu da suka balle daga Ukraine, na ceto su daga abun da suka kira "ci gaban harin sojojin Ukraine a kan al'umma".

A shafinsa na Twitter, ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba, ya wallafa cewar: Rasha ta kaddamar da yaki gadan gadan, ta hanyar hare hare a biranen Kiev, kuma kasarsa za ta kare kanta cikin nasara.

Ukraine Konflikt | Rauchwolke über Militärflughafen in Chuguyev
Hayaki a filin saukar jiragen sojin ChuguyevHoto: Aris Messinis/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Kiev babban birnin kasar Ukraine din dai na nuni da cewar, an ji karar jiniya da sanyin safiyar yau, kana ministan tsaron kasar ya sanar da cewar, dakarun Rasha na lugudan wuta a kan sansanonin sojin da filayen saukar jiragen sama da ke yankin gabashin Ukraine.

Amma ya ce sojojinsu na kokarin yin martani kan somamen na sojin Rasha ta sararin samaniya. Sai dai wasu rahotanni sun karyata saukar mayakan na Rasha a yankin Odessa.

A halin da ake ciki yanzu haka dai, sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da takwaransa na tsaro Lloyd Austin sun tuntumi babban sakataren Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO Jen Stoltenberg, kan irin martani da kawance za ta yi wa Rashan bisa mamayen Ukraine.