1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya sanya Obama yake jan kafa kan kasar Siriya?

September 3, 2013

Banbancin ra'ayi tsakanin kasashen Larabawa ya tilastawa shugaban Amirka Barack Obama tunani mai zurfi kafin ya dauki matakin kaiwa Siriya harin soja

https://p.dw.com/p/19bZA
Hoto: Kristoffer Tripplaar-Pool/Getty Images

Watakila yau, ko mako mai zuwa ko watakila nan da wata guda. Wannan dai shine yadda shugaban Amrika, Barack Obama ya baiyana shirye-shirynsa na kaiwa kasar Siriya harin soja. Shugaban ya yi wannan bayanin ne ranar Asabar, lokacin da yake gabatar da kudirinsa na amfani da karfin makamai domin ladabtar da shugaban Siriya, Bashar al-Assad, to amma yace zai jira amincewa daga yan majalisar dokokin kasarsa tukuna. Yan majalisar zasu duba batun na Siriya ne bayan sun kammala hutun lokcin bazara a ranar tara ga watan Satumba.

To daga baya, shugaba Barack Obama ya sassauta jawabansa a game da yiwuwar kaiwa kasar ta Siriya harin soja nan gaba kadan. Yace Amirka babu wani karfin soja da zata iya amfani dashi domin kawo zaman lafiya a kasar ta Siriya ko kuma sassauta mummunan halin da al'ummar kasar farar hula suke ciki. Bugu da kari kuma, an zabe shi ne saboda alkawarin da yayi na kawo karshen yake-yaken da Amirka ta shiga tsawon shekaru 10.

Sai dai kuma wannan kudiri na Obama ba zai rasa dangantaka da alamun da ya rika gani daga yankin gabas ta tsakiya ba. Alal misali, kasashen Saudi Arabiya da Qatar, wadanda suka fi kusantar Amirkan a adawar su kan gwamnatin Bashar al-Assad, a baya-bayan nan sun nuna dari-dari, inji masanin siyasa, Josef Janning na cibiyar kula da dangantaka da kasashen ketare ta Jamus, lokacin hira da DW.

Bashar Assad Präsident Syrien ARCHIVBILD 2010
Shugaban Siriya, Bashar al-AssadHoto: picture-alliance/dpa

"Yace duka kasshen biyu basa son ganin sun zama saniyar ware tsakanin ra'ayoyin sauran kasashen Larabawa a yankin, dake nuna rashin kaunar ganin Amirka tayi shisshigin soja a kasar ta Siriya. Saboda haka ne basa son baiwa Amirka goyon baya kai tsaye. Kasashen biyu ba zasu iya tafiyar da irin wannan siyasa ba. Amirka kuma tilas ne ta kula da matsayin kasshen Larabawa na son sulhunta matsalolinsu da kansu da kuma bukatun hana fadi-tashi a kasa kamar Saudi Arabiya."

Mafi yawan kasashen Larabawa suna adawa da nunawa gwamnatin shugaba Assad na Siriya karfin soja. Masu adawa da irin wannan mataki suna korafin cewar a duk lokacin da kasashen yamma suka so shissgigin soja a wata kasa, sukan bada dalilin yin hakan ne wai saboda ceto jama'a daga halin kaka-ni-kayi, kamar yadda aka gani a matakan su na soja a yankin, har ya zuwa kasar Irak a baya-bayan nan, inji Mustafa Zein na jaridar al-Hayat, wanda ma a sharhinsa, yace duk wani hari na soja, babu abin da zai haifar illa kara shigar da al'ummar farar hula cikin karin wahaloli. Kasashen democradiya na yamma, inji shi, mu suna kashemu, wai da sunan kare al'ummarsu.

Bisa lura da ra'ayoyin da suka banbanta a yankin na gabas ta tsakiya, ya zama wajibi ga Amirka ta rika sara tana duban bakin gatarinta, kamar yadda Markus Kaim na cibiyar kula da dangantaka da kasashen ketare ta Jamus ya nunar lokcin hira da DW.

"Yace a hannu guda suna samun cikakken goyon baya daga kasashe masu yawa na duniyar Larabawa a matakan da suke son dauka kan Siriya. A daya hannun kuma, tilas ne Amirkawan su yi kokarin kaucewa zaton nan cewar yan mamaye na kasashen yamma ko kuma kasashen da suka taba yiwa wannan nahiya mulkin mallaka, burinsu shine su sake maida al'ummar yankin na gabas ta tsakiya yan amshin shata ko kuma talakawan su da basu da yanci ko hakki. A daura da haka, yana da muhimmanci Amirkawan su nunawa duniya cewar kokarnsu na aukawa kasr Siriya ba zasu aiwatar dashi ne domin cima burin su ba, amma sai domin ganin Siriya din ta saba dokokin kasa da kasa da suka hana amfani da makamai masu guba."

Syrien Arabische Liga Sondertreffen
Taron koli na musaman na Kungiyar Hadin Kan Larabawa kan SiriyaHoto: Reuters

Ita kanta Siriya din di tana ci gaba da musunta amfani da irin wadannan makamai, inda kamfanin yada labarai mallakin hukuma, wato SANA yace wannan zargi ba komai bane illa propagandar yan tawayen kasar. Kakakin hadin gwiwar kungiyoyin yan tawaye, kuma jakadansu a Faransa, Monzar Makhous yace Amerika tana da yancin kaiwa Siriya harin soja, bisa dacewa da sharuddan Majalisar Dinkin Duiya, wadda alhakinta ne ta kare jama'a idan gwamnatin dake mulkinsu ta kasa wajen yin haka.

Mawallafi: Knipp/Umaru Aliyu
Edita: Abdourahmane Hassane