1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Kamfanonin Jamus su karkata Afirka

Yusuf Bala Nayaya
October 30, 2018

Merkel ta bayyana haka ne a wajen taron zuba jari a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus wanda ke zama wani bangare na kawancen kasuwanci tsakanin kasashen na Afirka da Jamus.

https://p.dw.com/p/37Niz
Deutschland Afrika-Gipfel bei Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga kamfanonin Jamus su karkata akalarsu daga yankin Asiya zuwa Afirka inda ta ce akwai damarmaki na tattalin arziki da dama a nahiyar, wadanda za su taimaka wajen rage 'yan gudun hijira da ke barin kasashen zuwa nahiyar Turai.

Merkel ta bayyana haka ne a wajen taron zuba jari a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus wanda ke zama wani bangare na kawancen kasuwanci tsakanin kasashen na Afirka da Jamus karkashin shirin nan mai lakabin "Compact with Africa" wanda Jamus ta kaddamar a lokacin jagorancin kasashe 20 masu ci gaban masana'antu.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta bayyana cewa abun farinciki ne ga kasashen Turai cewa kasashen na Afirka na da kyakkyawar makoma kamar yadda ta bayyana a taron na Berlin wanda Shugaba Paul Kagame na Ruwanda da Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ke cikin mahalartan sa.