1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kai ziyara Saudiyya

April 30, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka birnin Jiddah domin tattaunawa da mahukuntan Daular Saudiyya kan batutuwa da suka kama daga yaki da kungiyar IS da kuma dumamar duniya.

https://p.dw.com/p/2c9kY
Saudi-Arabien Merkel neben König Salman im Königspalast
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka birnin Jiddah domin tattaunawa da mahukuntan Daular Saudiyyar kan batutuwa da suka kama daga yaki da kungiyar IS da kuma dumamar duniya.

Ziyarar ta yini daya na zuwa ne yayin da Merkel ke kara kaimi na matakan diflomasiyya gabanin taron kungiyar G20 ta kasashe masu cigaban masana'antu na duniya wanda Jamus za ta karbi bakuncinsa a bana.

A ranar litinin kuma shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta wuce kasar hadaddiyar daular larabawa inda za ta gana da yarima Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan sannan ta gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi a ranar Talata.

Merkel za ta bukaci yin matsin lamba ga saudiyya ta sassauta matakinta kan shingen cinikayya. Yayin da a waje guda kuma ake sa ran za ta tabo batun kare hakkin dan Adam da gudunmawar mata tare da Sarki Salman da kuma yarima Mohammed bin Nahyan