1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi alkawarin taimakawa Macron

May 8, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin taimakawa zababben shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ta fuskar samarwa faransawa ayyukan yi.

https://p.dw.com/p/2cbtY
Russland | Pressekonferenz Merkel Putin
Hoto: Getty Images/AFP/A. Nemenov

Angela Merkel ta fadi hakan ne lokacin da ta ke wa Mr. Macron barka da samun nasara gagaruma a babban zaben Faransa, ta kuma ce Jamus da Faransa za su yi aiki tare wajen tabbatar da daidaito a nahiyar Turai. A jawabin da ta yi ranar Litinin a birnin Berlin, Merkel ta yaba tsayuwar Mr. Macron wajen bayyana manufarsa ta kare muradu da kuma bunkasar arzikin nahiyar Turai lokacin yakin neman zabensa.

Haka nan ta ce dangantakar manyan kasashen na Turai, babban ginshiki ne a tsarin alakar Jamus da kasashen ketare musamman kan batutuwan da suka shafi hulda ta amana tsakaninsu. Tuni ma dai Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana ranar Lahadin da ke tafe, a matsayin ranar da za a rantsar da zababben shugaban kasar Emmanuel Macron.

Shi dai Mr. Macron, ya yi nasara ne a zaben kasar kan abokiyar takararsa Marine Le Pen a ranar Lahadi, zaben da ya sami marhabi daga tarayyar Turai da shugabannin manyan kasashe.