1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da tsaurara dokokin mafaka a Jamus

Mohammad Nasiru AwalOctober 1, 2015

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta tabka mahawara game da yi wa dokokin ba da mafakar siyasa a kasar kwaskwarima.

https://p.dw.com/p/1GhQf
Deutschland Bundestag Asylrechtsänderung Thomas de Maizière
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya yi kira da a takaita yawan 'yan gudun hijira da za a karba a kasar. Ministan ya fadi hakan ne lokacin mahawara a majalisar dokoki ta Bundestag kan yi wa 'yancin samun mafakar siyasa a Jamus kwaskwarima, inda ya yi kira da a tsaurara dokokin tare kuma da gaggauta duba takardun 'yan gudun hijira.

"Daga cikin matakan da muke shirin dauka sun hada da: duk wanda ya ki komawa gida bayan an yi watsi da bukatunsa na neman mafaka, za a janye masa 'yancin samun wani tallafi da aka tanadar wa 'yan gudun hijira, in ban da muhimman abubuwa na bukatun yau da kullum."

A lokaci daya kuma gwamnatin Jamus na duba yiwuwar fadada matakan shigar da bakin cikin al'ummar kasar, musamman ma wadanda ke da kyakkyawar damar samun izinin ci gaba da zama a kasar.