1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus ya fara rangadi a Gabas Ta Tsakiya

February 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8M

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya tashi zuwa Isra´ila matakin farko a rangadin da zai kaiwa yankin GTT, inda zai gana da shugabannin Bani Yahudu da na Falasdinawa bayan lashe zaben da kungiyar Hamas ta yi. Ministan zai tattauna game da shirin nukiliyar Iran da ake takaddama a kai sai kuma dangantaka tsakanin Israi´ila da Falasdinu bayan zaben da ya dora Hamas kan mulki. Ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta ce ba´a shirya wata ganawa tsakanin ministan da jami´an Hamas ba. Baya ga Isra´ila da yankunan Falasdinawa Steinmeier zai kuma ziyarci kasashen Jordan da Turkiya.