1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Saudiyya na tunanin sake gina Falasdinu da yaki ya rugurguza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 21, 2024

Yarima Faisal bin Farhan, ya isa birnin Alkahira na Masar a wannan Alhamis, don tattauna hanyoyin sake gina yankunan Falasdinawa da yaki ya rugurguza

https://p.dw.com/p/4dyVm
Hoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, ya isa birnin Alkahira na Masar a wannan Alhamis, don tattauna hanyoyin sake gina yankunan Falasdinawa da yaki ya rugurguza.

Karin bayani:Za a koma kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza

Tuni shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa birnin na Alkahira, don tattauna yadda za a lalubo hanyoyin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar rikicin Gaza, tare da shigar da kayan agaji a cikin Zirin, domin tallafa wa Falasdinawan da yunwa ta galabaitar.

Karin bayani:Jagoran Hamas Ismail Haniyeh ya isa Masar kan rikicin Gaza

Kasashen Amurka da Masar da Qatar ne dai suke jagorantar kokarin cimma sulhun da ake yi.