Ministocin tsaron kasashen Jamus da Mongoliya sun gana
October 20, 2018Talla
Tun da fari Ministar ta gana da takwaranta na Mongoliya da kuma mataimakin Firaministan kasar bayan ta ziyarci wani sansani da Sojojin Jamus suke horas da Jami'an tsaron Mongoliya wadanda ke aikin tsaro a Afghnistan, dama dai Sojojin kasashen biyu na wani aikin hadin gwiwa a Afghanistan tare da dakarun rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
A gobe Lahadi Ministar tsaron za ta ziyarci kasar Chaina don tattaunawa da shugabannin bangarorin tsaro a kasar.