1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin EU sun tattauna kan bakin haure

Ibrahim Ishaq RanoApril 20, 2015

Sakamakon karuwar mace-macen bakin haure 'yan Afirka a tekun Bahar Rum, ministocin tarayyar Turai sun kuduri aniyar tinkara wannan matsala.

https://p.dw.com/p/1FBLS
Luxbemburg EU Außenminister Krisentreffen Flüchtlinge Mittelmeer
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Lamarin dai ya ta'azzara tunanin mahankalta da ke neman makoma ta gari wajen kawo karshen matsalar mutuwar ‘yan ci-ranin a kokarin ketare tekun. Tun gabanin wannan lokaci Majalisar Dinkin Duniya na cikin wadanda suka magantu banda irin su kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Amnesty International, kan hatsarin da ke yawan faruwa ba kuma tare da samun agaji daga masu ceto ba. A ta bakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban ki- Moon, dole ne gwamnatin kowacce kasa ta nuna damuwa kan wannan al'amari, sakamakon iftila'in baya-bayan nan, na mutuwar fiye da mutane 900 a rana guda.

Matakin dakatar da aukuwar wannan bala'i

Luxemburg dai ta dauki manyan baki da suka kasance mahukunta a tarayyar Turai irin su ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, da sakataren harkokin wajen Burtaniya Philip Hammond, da kuma shugabar kula harkokin ketare na tarayyar Turai Federica Mogherini, wadda ma ta yi nuni da cewa.

Symbolbild - Flüchtlingsboot Mittelmeer
Hoto: Marco Di Lauro/Getty Images

“Bayan abin da ya faru a daren Lahadi na ji a jiki na cewa wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyanmu domin mu dakatar da aukuwar irin wannan tashin hankali daga sake faruwa. Sanin kowane an zo gabar da ba za a iya yin uzuri ba, kuma gashi dai mun hadu, dukkanmu ministocin harkokin waje da ma na cikin gida, kuma za mu cimma nasarar kawo karshen matsalar 'yan ci-ranin a wannan lokaci."

Kafin ta'azzarar wannan matsala dai akwai jami'an tsaro na ruwa da ke karkashin kasar Italiya da aka yi ta takaddama a kan aikinsu, wajen danganta shi da yi wa masu tsallako iyakar jagora zuwa yankunan Turai ba bisa ka'ida ba. A dalilin haka a watan karshen shekarar da ta gabata, tarayyar Turan ta soke aikin na su, da bangarorin al'umma da dama suka yi imanin cewa shi ne babban ginshikin kai agajin gaggawa da ceto wadanda ke samun hadari irin wannan a yankin tekun na Bahar Rum ko kuma tsibirin Lampedusa.

Babban kalubale ga Turai

Karkatar akalar wannan zama na mahukuntan tarayyar Turai a wannan Litini ya biyo bayan tunanin wasunsu na cewa akwai babbar matsala game da wancan hukunci, kuma zaman yana nuni da cewa za a iya kamo bakin zaren warware matsalar ko da ba a gaggauce ba, wala-Allah wajen dawo da wancan aikin ceto zalla na sojojin ruwan Italiya, musamman ta la'akari da irin kalaman da ke fita daga bakunan irin su ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier.

Pressebilder MOAS EINSCHRÄNKUNG
Hoto: MOAS/Darrin Zammit Lupi

"Muna fuskantar babban kalubale, ina so a sani cewa babu yiwuwar kawo karshen matsalar cikin gaggawa, amma dai mun yin jimamin halin rayuwar wadanda abin ya shafa da 'yan uwansu. Sannan za mu dauki mataki nan kusa, domin kawo karshen mutuwar 'yan ci-ranin a tekun na Bahar Rum."

Kari a kan wannan ma shi kansa shugaban majalisar tarayyar Turai Martin Schulz cewa ya yi.

"Ba za mu iya ci gaba da zama a wannan hali ba tare da mun yi wani abu ba. Muna bukatar kyakkyawan tsari na doka a kan bakin haure da ke shigowa. Irin wannan zama mun yi shi shekaru 20 da suka gabata, amma babu abin da ya canja, illa ma yawan mutuwar jama'a. A don haka ina rokon mu kasashen Turai, da mu dauki matakin gaggawa yanzu yanzu."

Hadarin na baya-bayan nan dai kamar yadda rahotanni suka nuna ya auku ne a dalilin kifewa da kwale-kwalen ya yi lokacin da fasinjoji suka tattaru a gefe guda, saboda yunkurinsu na tsallakawa su shiga wani babban jirgin ruwa da ke kusantar su. Kawo yanzu adadin wadanda suka mutu ya doshi 1500 a iya wannan shekara.

Bayan matakai da tarayyar Turan za ta dauka kan wannan al'amari, ita kanta kasar Italiya lokacin wani taron gaggawa da Faraminista Matteo Renzi ya kira jim kadan bayan aukuwar wancan iftila'i, ta shirya aikin ceto karkashin hurumin yin amfani da jiragen ruwa kimanin 20, da kuma wasu jirage uku masu saukar ungulu.