1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU na yin taro kan batun bakin haur

Abdourahamane Hassane
July 12, 2018

Ministocin harkokin cikin gida na kasashe 28 na kungiyar tarrayar Turai za su soma gudanar da wani taro a birnin Innsbruck da ke a kudancin Austriya

https://p.dw.com/p/31Jlf
Bundeswehreinsatz im Mittelmeer
Hoto: picture alliance/dpa/Bundeswehr/PAO Mittelmeer

Taron wanda shi ne za a yi a karon farko a karkashin jagorancin Austriya da ta karbi ragarmar kungyar ta EU. Zai tantance matakan da aka tsayer cikin sabani tsakanin kasashen na mayar da 'yan cirani zuwa Afirka wadanda aka ceto daga tekun Bahrum. Daga cikin ministocin har'da na Jamus Horst Seehofer wanda ya kalubalanci shugabar gwamnatrin Jamus a game da batun 'yan ci rani a rjejeniyar da suka cimma a makon jiya.