1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sulhu da 'yan tawayen Renamo ya dauki hankali

Mohammad Nasiru Awal
August 9, 2019

Bisa ga dukkan alamu a wannan karo yarjejeniyar zaman lafiya za ta dore tsakanin 'yan tawayen Renamo da gwamnatin Mozambik yayin da bangarorin biyu suka jaddada kudirin cika alkawuran da suka dauka.

https://p.dw.com/p/3NeQi
Friedensvertrag Mosambik
Hoto: DW/A. Sebastião

A sharhinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce kimanin wata guda gabanin ziyarar da aka shirya Paparoma Francis zai kai Mozambik, watanni biyu kuma gabanin zabukan 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa, shugaban Mozambik Filipe Nyusi na jam'iyyar Frelimo da jagoran 'yan tawayen kungiyar Renamo da ta rikide ta zama babbar jam'iyyar adawar kasa, Ossufo Momade sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin da kasar ta kwashe shekaru gommai tana yi. Yarjejeniyar da ke zama irinta ta uku da bangarorin biyu suka taba kullawa, ta biyo bayan tattaunawa ta tsawon shekaru tun gabanin mutuwar tsohon jagoran kungiyar Renamo Afonso Dhlakama a watan Mayun 2018. Jaridar ta ce ganin yadda mayakan 'yan tawayen Renamo suka dukufa wajen rajistar sunayensu, suna kuma kwance damarar yaki, ita kuma gwamnati ta ba da tabbacin cika alkawuran da ta dauka, bisa ga dukkan alamu a wannan karo yarjejeniyar za ta dore.

Yaki da Ebola na ci gaba da daukar hankali

Annobar cutar Ebola a kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus. A labarin da ta buga mai taken, "Yankin da a dole likitoci ke rike makamai" jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce duk da duk dubban ma'aikatan agaji da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya, har yanzu ana samun sabbin masu kamuwa da kwayoyin cutar Ebola a Kwango. Jaridar ta ce sau da yawa al'umma ba sa yarda da jami'an kiwon lafiya bisa zargin cewa gwamnati da baki 'yan agaji ba sa kawo wani abin kirki. A tsakiyar watan Yuli Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta ayyana dokar ta-baci a yankin gabashin Kwango, inda kawo yanzu aka yi rajistar mutum 2700 sun harbu da kwayoyin cutar yayin da fiye da 1800 suka kwanta dama. Jaridar ta ce a wani lamari mai kama da ana magani kai na kaba, duk da dubban ma'aikatan agaji da cibiyoyin kiwon lafiya da allurar riga kafi da aka kai yankin, cutar na barazanar bazuwa zuwa wasu yankunan.

Matsalar 'yan fashin teku a mashigin tekun Gini

A labarin da ta buga dangane da matsalar fashin teku, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara sharhinta ne da cewa 'yan fashin teku sun janyo rashin tabbas a mashigin teku Gini, tana mai cewa a halin yanzu sama da kashi 90 cikin 100 na garkuwa da jiragen ruwa na faruwa ne a yammacin Afirka a daidai lokacin da wannan matsala ta yi sauki a gabar tekun kasar Somaliya. Jaridar ta ce tun farkon wannan shekara an yi garkuwa da matukan jiragen ruwa 62 a yankin na mashigin tekun Gini, baya ga fashin da ake wa jiragen da jaridar ta ce yana karuwa, musamman a kusa da gabar tekun Najeriya. Ko da yake a 2013 kasashen yankin sun kulla yarjejeniyar inganta aikin tsaron tekun amma har yanzu kowacce a cikinsu na yin gaban kanta maimakon hada karfi waje guda don yakar matsalar fashin tekun, inji jaridar