1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe ya gana da kwamandan da ya tsare shi

Yusuf Bala Nayaya
November 16, 2017

A ranar Alhamis din nan an gano Shugaba Robert Mugabe na ganawa da kwamandan sojoji da ya sanya shi cikin talala a gidansa, da ma jakadun kasar Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/2nloo
Simbabwe Constantine Chiwenga und Robert Mugabe
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Hakan dai na zuwa bayan da wakilai daga Afirka ta Kudu da manyan malaman majami'a daga darikar Katolika suka zauna don duba turka-turkar da ke neman daurin gwarmai ga makomar gwamman shekaru na mulkin Mugabe a Zimbabuwe.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu a lokacin da yake jawabi ga 'yan majalisa ya ce nan ba da dadewa ba za a warware matsalar da kasar ta Zimbabuwe ta shiga.

Su kuwa kungiyoyi masu zaman kansu da 'yan adawa sun aza kaimi wajen kira ga Mugabe ya ajiye mulkin kasar bayan shekaru 37 ta yadda za a samu damar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali. Babu dai labarin dawowar mataimakin shugaban Emmerson Mnangagwa wanda korarsa ta hargitsa kasar da ma sanya tunzurin soja su yi kane-kane kan harkokin mulki duk da cewa sun ce ba juyin mulki suka yi ba.