1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe ya kare nasarar jami'yyarsa

August 12, 2013

Robert Mugabe na Zimbabwe ya ce duk wani yunƙuri na sauya nasarar da jamiyyarsa ta ZANU-PF ta yi, ba zai saɓu ba, tunda masu sanya ido daga Afirka sun amince da shi

https://p.dw.com/p/19O7h
Zimbabwe's President Robert Mugabe addresses the crowd gathered to commemorate Heroes Day in Harare August 12, 2013. Mugabe told critics of his disputed re-election to "go hang" on Monday, dismissing his rivals as "Western-sponsored stooges" at a liberation war commemoration that was boycotted by his principal challenger. The Movement for Democratic Change (MDC) of Mugabe's rival Morgan Tsvangirai filed a court challenge on Friday against the announced landslide win of Mugabe and his ZANU-PF party in the July 31 vote, alleging widespread rigging and intimidation. REUTERS/Philimon Bulawayo (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS HEADSHOT)
Robert MugabeHoto: Reuters

Daɗaɗɗen shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe ya ce babu yadda za a yi jamiyyarsa ta miƙa wuya ga duk wani yunƙuri na sauya nasarar da ta yi a zaɓukan ƙasar ba, inda ya ce duk da cewa ana ƙalubalantan sakamakon, masu sanya ido daga ƙasashen Afirka sun amince da shi, kuma sun ce zaɓe ne da aka gudanar ba tare da tashin hankali makamancin wanda ya afku a shekarun baya ba.

A jawabinsa na farko cikin bainar jama'a, tun bayan zaɓen na 31 ga watan Yuli, Mugabe ya tattauna batun zaɓen yayin taron shekara-shekara na tunawa da dakarun da suka rasu lokacin yaƙin neman 'yancin kan ƙasar a shekarar 1980.

Mai shekaru 89 ya haƙiƙance kan cewa al'umma ce ta zaɓe shi da san ranta ba tare da an tilasta mata ba. Babban abokin hammayarsa Morgan Tsvangirai wanda ke ƙalubalantar sakamakon a Kotu wanda kuma zargin an yi maguɗi a kowani mataki na zaɓen ya ƙauracewa wannan taron karrama tsoffin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya, duk da mahimmancinsa ga tarihin ƙasar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe