1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawa mai zafi kan manufofin harkokin wajen Amirka

October 23, 2012

Shugaban Amirka Obama da mai kalubalantarsa Romney, sun yi musayar kalamai kan manufofin harkokin kasashen ketere.

https://p.dw.com/p/16UoA
Hoto: Reuters

An gudanar da mahawa ta ƙarshe tsakanin 'yan takaran shugancin Amirka, inda aka fafata tsakanin Shugaba Barack Obama da mai adawa da shi Mitt Romney, kuma anfi mayar da hankali kan rawar da ƙasar za ta taka game da manufofin harƙoƙin ƙasashen ƙetere.

Duk da ya ke mahawarar ta uku kuma ta karshe, an shirya bisa manufofin harƙoƙin waje, duk 'yan takaran kan jefa maganar tattalin arziƙi da magance rashin aiki waɗanda su ne, za su fi jawo musu kuri'un Amirkawa.

Amma duk 'yan takaran sun nuna mahimmancin Amurka ga ƙasashen duniya, da yadda za su tafiyar da harƙoƙin gabas ta Tsakiya da cinikayya da China, gami da dangantaka da Rasha, da sauran ƙasashen duniya.

Ga yadda Mitt Romney ya bayyana yadda zai tunƙari sauyi da ake samu a ƙasashen Larabawa:

'Za mu saka cikekken tsari wanda zai taimaki ƙasashen Musulmai da sauran ƙasashe, su kawar da tsat-tsauran ra'ayi, saboda yadda yanzu su ka yadu cikin ƙasashe aƙalla 12 tare da kawo barazana. Kuma sun zama barazanar tsaro ga abokanmu da Amirka, domin haka, tilas mu samu shirin kawar da wannan tsat-tsauran ra'ayi.'

Amma a daya hanun, shugaba Barack Obama na Amirkan, ya bayyana yadda zai ci gaba nuna ba sani ba sabo kan harƙoƙin nukiyar Iran, tare da wasti da zargi nuna sako-sako:

'Wannan shi ne babban abun almara da ake fada cikin wannan yaƙin neman zabe, kuma Gwamna wannan ba gaskiya ba ne, idan ana maganar takunkumi, mun saka takunkumin da ya fi ko wanne tsauri.'

Duk yadda ta kasance ranar 6 ga watan gobe na Nowamba, Amirka za su tantance shugaba gaba tsakanin mutane biyu shugaba Barck Obama da Mitt Romney.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu