1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara game da korar baƙin haure daga Najeriya

January 7, 2013

A ƙoƙarin tabbatar da tsaro cikin ƙasa gwamnati Najeriya, ta ƙuduri aniyar korar dubunan 'yan ci rani na ƙasashen ƙetare.

https://p.dw.com/p/17FRg
Karte Nigeria englisch mit der Region Kaduna, der Hauptstadt Abuji und Jaji

A wani abinda ke nuna sauyi ga manufofin Najeriya a kan ƙudurin ƙungiyar Ecowas na bada izinin shige da ficen jama'a ba tare da wani cikas ba, Najeriyar ta ce ba zata iya bin wannan ƙuduri sau da ƙafa ba, saboda matsaloli na rashin tsaro.

Wannan mataki da ke zama wata sabuwar manufa da Najeriyar ta ɗauka a game da ƙudurin na ƙungiyar Ecowas ko CEDEAO wanda ya buƙaci kawar da duk shingayen da kan kawo cikas a kai da komowa a tsakanin ƙasashen juna, ƙuduri da ake wa kallon muhimmi ne a faɗi tashin da Ecowas ta daɗe tana yi na samun gamayya a tsakanin ƙasashen ƙungiyar.

Ko da yake ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriyar Abba Moro ya ce Najeriya na cikin wannan ƙuduri na Ecowas to sai dai ƙasar za ta ƙara sa ido sosai a kan baƙin da ke shiga ƙasarta, don haka ba zata iya bin wannan ƙuduri sau da ƙafa ba. Dr Faruq B.B Faruq, ƙwarre ne a fannin hulɗoɗin ƙasa da ƙasa da siyar duniya da ke jami'ar Abuja.

‘'A yadda ake tafiyar da al'ammura a yanzu tun kusan shekaru 300 da suka gabata ƙasashe sune su ke da martaba a tafiyar da abubuwa to Ecowas ta karya wannan ta kuma so ta yi hakan tun kafin turawa su yi nasu cewa zaka iya ɗage shinge tun da turawa ne suka sanya mana, to amma a tafiyar da gwamnatoci kuma akwai matsala. Amurka ta na da nata tsarin tana son ta zo ƙasashe irin su Mali, ta yi irin abubuwan da take yi a Afganistan to in ko an dage wannan shinge kaga mutane tattarowa zasu yi su fara zuwa kasashen da sukan san akwai tsaro''.

General picture of an ECOWAS Summit gathering west African leaders to plot a military strategy to wrest control of northern Mali from Islamist groups as fears grow over the risks they pose to the region and beyond, on November 11, 2012 in Abuja. West African plans could see the mobilisation of some 5,500 soldiers, essentially but not totally drawn from the region. Between 200 and 400 European soldiers will train troops in Mali, according to the operational plan. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Taron ECOWASHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Najeriya da ake wa kallon yaya babba a tsakanin ƙasashen da ke ,ƙungiyar ta Ecowas musamman wajen ƙoƙarin ƙarfafa ƙawance da ma gamaiyya a tsakaninsu, abinda kan sanya yan asalin ƙasashen Afrika da dama zama tamkar 'yan gida a Najeriyar, to sai dai tuni ake ganin sauyi, inda ya zuwa yanzu Najeriyar ta tasa ƙeyar yan ƙasashen waje har su dubu 16 abinda a lokutan baya ba kasafai ake ganin hakan ba.

Bisa la'akari da sakamakon da wannan sauyi ka iya haifarwa a kan wannan muhimmin kuduri na kungiyar ta Ecowas ya sanya tambayar tasirin da sauiyin da Najeriya bta yi ka iya yi a kan wannan lamari. To sai ga Malam Buhari Muhammad na cibiyar demokraɗiyya da ci gaban ƙasa na ganin Najeriyar ta baro shiri a kan wannan yunkuri da ake dangata shi da matsaloli na rashin tsaro.

‘'Don matsalar cin ha nci da rashawa ne day a yi yawa, amma bai kamata a ce an dauki irin wannan mataki ba, don ai muma muna shiga Niger kuma muna bin dokokinsu, suna barinmu mu shiga mu fita ba tare da wata matsala ba, amma mu namu cin hanci da rashawa ne da ya yi yawa shi ya sa ake barin mutane suna yin abinda suka ga dama. Tabbas ya kamata Najeriya ta nemi haɗin kan ƙasashen da ta ke zagaye da su, domin ina ganin muzgunawa a wannan lokacin ba shine abin yi ba''.

Abin jira a gani shine abinda zai biyo baya ga wannan mataki da Najeriya ta ɗauka da ƙwarru suka bayyana ya karya ƙa'idar wannan ƙuduri da ba kawai ya bukaci ƙasashen Ecowas su kawar da duk wasu abubuwa da ke kawo cikas a fannin kaida komowa jama'a da hajojinsa bane, har ma da ba su izinin zama da ma samun aikin yi a ƙasashen da ba na su ba waɗanda suke a ƙarƙashin ƙungiyar ta Ecowas

Soldier patrol to monitor protesters at Ojota district in Lagos on January 16, 2012. Nigerian security forces fired tear gas and shot into the air Monday to disperse around 300 protesters in Lagos as authorities moved to prevent demonstrations in various parts of the country. Nigerian unions announced on January 16 they were suspending a week-old nationwide strike over fuel prices which has shut down Africa's most populous nation and brought tens of thousands out in protest. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Kalubalen rashin tsaro dai da Najeriya ke fuskanta na ci gaba da yin tasiri a kan al'ammuran cikin gidan da ma hulɗoɗinta da ƙasashen waje da dama.

Mawallafa: Uwais Abubakar Idriss / Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal