1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan gagarumin albashin yan majalisun Najeriya

July 23, 2013

Cikin dan kankanen lokaci jijiyar wuya ta daga a Tarrayar Najeriya inda yanzu haka sabuwar muhawara ta balle game da babban banbancin samu dake tsakanin masu mulkin kasar da talakawan da suke ikirarin yiwa mulki.

https://p.dw.com/p/19DIy
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Babu dai zato ba kuma tsammani abun boye ya kai ga fitowa fili lokacin da ta wata mujallar birnin London tace  masu dokokin Tarrayar Najeriya na zaman mafiya jin dadi a daukacin duniya baki daya ga batun albashi da sauran alawus-alawus.

Mujallar da tace tayi bincike kan albashi dama alawus-alawus din da ‘ya'yan majalisun dattawa dana wakilan kasar ta Najeriya ke samu dai na nuna kowane dan majalisa na samun abun da bai gaza Naira Miliyan 30 ba  a matsayin gundari na alabashinsa duk shekara, banda kuma dimbin alawus-alawus irin na debi da kanka  da ya maida su na kan gaba ga batun samu a ko ina a duniya.

Yan majalisar dai a fadar mujallar Economist sun dara yan uwansu dake Japan  mai takama da karfi na tattalin arziki,da ma Amurka inda Tarrayar Najeriyar ke takamar koyon demokaradiyar ta a can , balle kasashe irinsu Ghana da Indiya de can baya ga batun samun na cefanen.

Tun a shekara ta 2007 ne dai hukumar tarawa da kuma rabon kudin kasar ta Najeriya ta fitar da wani sabon albashi na musamman  ga ‘ya'yan majalisun kasar biyu albashin kuma da tace na da burin kauda idon su cikin taba kayan al'umma a kasa.

Nigeria Blick über die Hauptstadt Abuja
Abuja, babban birnin Tarayyar NajeriyaHoto: Reuters

Kuma kokarin jin ta bakin hukumar dai ya ci tura a tsakanin shugabanta dake riko dama sakataren ta na riko da kowannensu ya shaida mun bashi abun fada a cikin sabon rahoton da yazo dai dai lokacin da kasar ke fuskanatar barazanar durkushewa sakamakon nauyi na kudi.

To sai dai kuma a fadar Senator Alkali Abdulkadir Jajere dake zaman daya daga cikin yan majalisar dattawan kasar da kuma ake zargi da amfana daga albashin dai akwai batu na karin gishiri a cikin matsayin.

Banbancin tsari kuma banbancin albashi dai, an dai dama dade ana korafi dama noke noke game da albashin masu dokar kasar ta Najeriya da ya nunka samun har sau 116.

 Abun da  kuma  a cewar Kolawole Banwo dake zaman daya daga cikin manyan jami'an kungiyar  farar hula ta Cislac dake bin diddigin harkokin majalisun dokokin kasar ya sanya yan majalisar suka dauki tsawon lokaci suna buyan samun nasu ga jama'a.

Zentralbank von Nigeria
Babban bankin Najeriya(CBN)

Tuni dai dama babban bankin kasar na CBN yayi korafinkisan kusan kaso daya a cikin hudu na kudaden tafi da harkokin yau da kullum a cikin zauren majalisun kasar biyu.

Abun kuma da ya tilasta wani ragin albashin a shekara ta 2011. Ragin kuma da ya gaza tasiri wajen sauyin rayuwa dama wandakar yan dokar kasar

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu