1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mukabala Tsakanin Bush Da Kerry

October 1, 2004

A yakinsu na neman zabe shugaba Bush ya fuskanci abokin takararsa John Kerry a wata zazzafar mahawarar da suka gudanar ta gidan telebijin Amurka

https://p.dw.com/p/Bvg3
George W. Bush da John Kerry
George W. Bush da John KerryHoto: AP

Daidai yadda aka tsammata tun farko mahawarar, wacce sama da mutane miliyan 50 suka yi bitarta ta gidan telebijin a kasar Afurka tayi zafi matuka ainun, inda akai-akai jami’an siyasar guda biyu suka batu da kakkausan harshe akan manufofin tsaro da na ketare. Shugaba Bush ya shiga kaka-nika-yi a yayinda aka tabo maganar Iraki. John Kerry yayi amfani da mawuyacin halin dake dada yin tsamari kusan a kullu yaumin a kasar ta Iraki domin sukan lamirin manufofin shugaba Bush. Ya ce Bush ya caba kuskure wajen gabatar da wannan yaki a wurin da bai da ce ba kuma a wani lokacin da bai dace ba. A nasa bangaren shugaba Bush ya dage ne akan kame-kame da ikirarin gazawar abokin takararsa sakamakon niyyarsa ta canza alkibla a game da rikicin Iraki. Amma fa a karo na farko a wannan babi na yakin neman zabe da aka shiga John Keryy ya bayyana hazakar da Allah Ya fuwace masa, ina bai yi wata-wata ba wajen yin nuni da cewar alamar gazawa fa shi ne idan mutum ya ki ya amince da kurakuransa ballantana a samu kafar yin gyara. Wani abin da aka lura da shi dangane da makabalar da gaggan jami’an siyasar suka yi shi ne na cewar da zarar ya cimma nasara John Kerry zai nemi ganin kawayen Amurka a nahiyar Turai sun kara karfafa rawar da suke takawa a siyasar duniya, ko da yake ba zai yi fatali da manufar kasar game da matakan kandagarki na soja ba. Kazalika bisa sabanin shugaba Bush, John Kerry na da niyyar tattaunawa kai tsaye da gwamnatin Koriya ta Arewa, lamarin da za a yi madalla da shi matuka da aniya. A takaice dai an lura da banbance-banbancen matsayin ‚yan takarar guda biyu dangane da maganar tsaro da yakar ta‘addanci, wacce ta fi ci wa jama’a tuwo a kwarya, ba ma kawai a kasar Amurka ba har da sauran sassa na duniya. Daga baya-bayan nan dai akasarin al’umar Amurka sun fara tababa a game da manufofin shugaba Bush to sai dai John Kerry bai ankara da hakan ba ballantana yayi amfani da wannan dama a yakinsa na neman zabe. Mai yiwuwa mukabalar ta gidan telebijin ta kasance wani matakin farko a gare shi domin ba wa yakin neman zaben wani sabon fasali akan manufa.