1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmai mabiya Shiya sun yi bikin Ashura

November 25, 2012

Miliyoyin Musulmai mabiya ɗarikar Shiya sun halarci bikin Ashura a wannan Lahadi a garin Karbala na ƙasar Iraki.

https://p.dw.com/p/16pZE
Hoto: picture-alliance/dpa

Miliyoyin Musulmai mabiya ɗarikar Shiya sun halarci bikin Ashura a wannan Lahadi a garin Karbala na ƙasar Iraki.

Wannan shi ne biki mafi girma na mabiya ɗarikar ta Shiya, inda su ke tafe su buga hanu a jikin ƙirji, domin tunawa da kisan da aka yi wa Imam Hussein, jikan Annabi Mohammadu, cikin shekara ta Jihara 680, kisan da dakarun da ke biyayya wa Khalifa Yazid su ka aiwatar.

A cikin shekarun da su ka gabata, bukukuwan sun gamu da hare hare da su hallaka mutane masu yawa.

A wani labarin mai nasaba da wannan, aƙalla mutane biyar sun hallaka, yayin da wasu kusan 90 su ka samu raunika, sakamakon harin bam akan Musulmai mabiya Shiya a garin Dera Ismail Khan na ƙasar Pakistan a wannan Lahadi.

Tuni 'yan sanda su ka tabbatar da faruwar lamarin, yayin da gwamnati ke ci gaba da ɗaukan matakan shawo kan hare haren da tsagerun Musulmai mabiya Sunni ke kaiwa kan tsirarun al'ummomin ƙasar.

Hukumomin ƙasar ta Pakistan, sun taƙaita yawan ababen hawan da ke kaiwa wuraren da 'yan Shiyan ke gudanar da bukukuwan Ashura, da zumma shawo kan hare haren.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas