1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi za su yi aikin Hajji a bana

April 10, 2022

Bayan kwashe shekaru biyu ba tare da samun damar aikin Hajji ba a duniya, Saudiyya ta sanar da cewa a bana za a koma muhimmin aikin da ake girmamawa a addinin Islama.

https://p.dw.com/p/49hu4
Saudi Arabien | Pilger an der Kaaba in Mekka
Hoto: ABDEL GHANI BASHIR/AFP/Getty Images

Saudiyya ta ce za ta bai wa Musulmi miliyan guda daga ciki da ma wajen kasar damar aikin Hajji a bana, damar da ake gani ta farko tun bayan bazuwar annobar corona a duniya.

Sai dai hukumomin kasar sun ce wadanda za su yi aikin Hajjin da za a yi cikin watan Yuli a banan, dole ne su kasance 'yan kasa da shekaru 65 da haihuwa, kuma sun samu cikakkun alluran rigakafin corona.

Shekaru biyun da suka gabata ne dai aka yi matukar rage adadin mahajjata saboda gudun barazanar annobar ta corona.

A baya dai Musulmi akalla miliyan biyu da dubu 500 ne ke aikin na Hajji daga ko'ina a duniya, daya daga cikin shika-shikan addinin Islama.

Ana dai kwadaita wa Musulmi baligi da ke da karfi da cikakkiyar lafiya, da ya yi aikin na Hajji akalla sau guda a rayuwarsa.