1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 14 sun mutu a harin Lahore

Zainab Mohammed AbubakarMarch 15, 2015

'Yan Taliban na kasar Pakistan din ne dai suka dauki alhakin hare-haren da aka kai a wasu majami'u guda biyu lokacin da ake addu'ar Lahadi a garin Youhanabad.

https://p.dw.com/p/1ErAA
Pakistan Anschläge auf Kirchen in Lahore
Hoto: picture-alliance/dpa/I. Sheikh

Mutane 14 suka mutu kana wasu sama da 70 suka jikkata, a harin kunar bakin wake da 'yan Taliban suka kai a wasu majami'u biyu a birnin Lahore na Pakistan. Harin dai ya jagoranci barkewar tarzomar da ta yi sanadiyyar rayukan wasu da ake zargin masu tsananin ra'ayi ne guda biyu.

A wani abun da ba'a taba ganin irinsa ba, mabiya addinin christa wajen 4,000 suka yi bore a kan titin wannan birni da ke yankin gabashin Pakistan. Masu boren na dauke da sanduna da suka rika rusa motoci da wasu gine-gine da ke tashar motar garin, a wani mataki na nuna bacin ransu.

Jami'an kasar sun shaidar da cewar an kai harin ne a wasu Majami'u guda biyu da ke makwabtaka da juna, a daidai lokacin da ake adduo'in, a garin Youhanabad da ke da mabiya addinin christa kimanin dubu 100.

Dr Mohammad Saeed da ke jagorantar babban asibitin garin, ya ce an kawo musu gawarwakin mutane 14,banda maharan da wadanda aka kashe, a yayin da wasu 70 ke samun jinya a yanzu haka.