Mutane 17 sun rasu a tashin hankali a arewacin Najeriya
April 29, 2013Wani jami'in soji a tarayyar Najeriya ya ce an halaka akalla mutane 17 a wani fada da aka gwabza tsakanin 'yan bindiga da dakarun tsaro a yankin arewa maso gabacin tarayyar ta Najeriya. An gwabza fadan ne a garin Bama dake a jihar Borno, inda tun a shekarar 2010 'yan bindiga ke fafatawa da dakarun gwamnati. Laftanan Kanal A.G. Laka ya fada a wannan Litinin cewa fadan yayi sanadiyar mutuwar jami'an 'yan sanda bakwai da kuma 'yan bindiga 10. 'Yan jarida da ke wa wata tawagar gwamnati rakiya a yankin sun ce ba su ga gawa ko guda daya ba, sai dai sau da yawa sojoji a Najeriya na rage yawan wadanda irin wannan tashin hankali kan rutsa da su. Wani dan jarida ya ce an kona gidaje da kuma shaguna da kuma wuraren kasuwanci.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar