1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 8 sun mutu a hare-hare a Somaliya

Abdul-raheem Hassan MAB
June 15, 2019

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutane da dama a Somaliya babban birnin kasar Somaliya. Tuni 'yan ta'adda na al Shabaab sun dauki alhakin hare-haren.

https://p.dw.com/p/3KWtv
Somalien Bombenanschlag in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Mayakan al-Shabaab sun dauki alhakin harin kunar bakin wake da ya kashe mutane akalla 8 tare da jikkata wasu da dama a kusa da ginin majalisar dokokin kasar a wannan Asabar. Wadanda suka shaidar da harin na cewa bam din ya rusa shaguna da gidajen mutane da dama. Rahotanni sun ce an kuma samun tashin wani bam a babban titin zuwa filin jirgin sama da ke babban birnin kasar Mogadishu, Sai dai babu rahotannin asarar rayuka a harin na biyu. 

'Yan sanda sun killace dukkannin titunan da suka hade da wurin da aka kai hare-haren, jami'an agajin gaggawa kuma na ci gaba da ayyukan ceto. Tun dai ba yau ba mayakan al-Shabaab da ke ikirarin zama reshen kungiyar al-Qa'ida na zama barazana ga rayuwar fararen hula tun bayan da kungiyar ta lashi takobin ganin bayan gwamnati.