1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu a Maiduguri

Gazali Abdou TasawaOctober 16, 2015

Wasu 'yan kunar bakin wake ne suka tayar da bama-baman da ke jikinsu cikin masallacin anguwar Mola na Maiduguri a lokacin sallar magariba

https://p.dw.com/p/1Gp8w
Nigeria Anschlag in Gombe
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu shaidun gani da ido sun ce 'yan kunar bakin wake ne su biyu da suka shigo masallacin cikin tufafi na musulmi inda daya ya fara tayar da bam din da ke a jikinsa kafin na biyu shima ya tayar da nashi a daidai lokacin da jama'a ke kokarin bada agaji ga wadanda harin farkon ya rutsa da su a dai dai lokacin da ake shirin sallar magariba .Wani shima da ke kusa da masallacin lokacin abkuwar lamarin ya ce ya kirga gawarwaki 42 na mutanen da suka halaka a cikin harin.

Hukumomin 'yan sanda na birnin na Maiduguri sun tabbatar da kai harin sai dai sun ce mutane 14 ne suka mutu a cikin. Tashin bam din ya ruguza ginin masallacin wanda ya taushe tarin masallata inda da dama daga cikinsu suka ji raunuka.