1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da tserewa kudancin Siriya

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2018

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a Jordan, ta ce zafafa hare-haren dakarun gwamnati na tsananta fitar mutane a Kudu maso yammacin Siriya.

https://p.dw.com/p/30gLb
Syrien Angriff auf Daraa
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Nabaa Media

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu 160 ne suka bar muhallansu cikin makonni biyu bayan fara kaddamar da hare-haren kwace iko da kudancin kasar daga hannun 'yan tawaye, mutanen na samun mafaka a yankunan da ke kusa da iyakar Isra'aila da Jordan, sai dai Isra'ila ta killace kan iyakarta.

A yanzu dai MDD na nuna fargabar tsananin mawuyacin hali da jama'a za su shiga sakamakon rashin shiga da kayan agaji yankunan da ake kai hare-haren, amma ministan harkokin wajen Jordan Ayman al-Safadi ya ce zai tattauna batun tsagaita wuta a ziyarar da zai kai kasar Rasha domin ba wa kungiyoyin agaji damar kai agaji ga dubban fararen hula.