1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar daruruwan mutane a kurkukun Najeriya

Uwais Abubakar IdrisOctober 15, 2013

Ana fara maida murtani a game da rahoton Amnesty International da ke cewa fiye da mutane 950 sun mutu a lokacin da sojojin Najeriyar ke tsare da su bisa zargin alaka da kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1A0Nh
epa03701818 Nigerian soldiers fire rifles on a shooting range in Bauchi, Nigeria, 15 May 2013. Nigerian President Goodluck Jonathan (not pictured) on 14 May 2013 declared a state of emergency in three north-eastern Nigerian states hardest hit by the radical Islamist Boko Haram insurgency. More security forces would be deployed to these areas to flush out Islamist insurgents, but all political office holders in the three states would remain in office, Jonathan said on 14 May. EPA/DEJI YAKE +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan rahoto na kungiyar kare hakin jama'ar ta Amnesty International ya sake bankado irin mumunan halin da ake tsare da dubban daruruwan mutanen da sojojin Najeriyar ke tsare da su a wuraren tsare jama'a daban-daban saboda an kamasu da zargin suna da alaka da kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awatti Waljihad wato Boko Haram.

Abin da ya fi daga hankali shi ne yadda kungiyar ta Amnesty International ta ce sahihin bayanin da ta samu daga wani babban jami'in sojan Najeriyar ya tabbatar da cewar mutane fiye da mutane 950 suka mutu a hannun sojojin a cikin watanni shida kadai na wannan shekarar ta 2013. Wannan ya kara haifar da zargin da kungiyoyin kare hakin jama'a suka dade suna yi a kan rashin sanin zahirin halin da ake tsare da irin wadannan mutanen da ake zargi a kasar.

Dole ne a yi bincike a hukunta masu laifi

An officer of the Joint Military Task Force (JTF) patrol in the northeastern Nigerian town of Maiduguri, Borno State , on April 30, 2013. Fierce fighting between Nigerian troops and suspected Islamist insurgents, Boko Haram at Baga town in the restive northeastern Nigeria, on April 30, 2013 left dozens of people dead and scores of civilians injured. But the military denied the casualty figures claiming it was exaggerated to smear its image. Meanwhile normalcy has return to the town as residents are going about their normal business. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Mr Kola Banwo na kungiyar kare hakin jama'a ta Cicilac ya ce ba za su lamunci wannan ba kuma dole ne a yi bincike.

"Wannan ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ba ta yi abinda ya kamata ba domin an san dai za a kama mutane kuma mutanen nan sai an kai su gaban alkali an yanke masu hukuncin da ya kamata ba za a ce sun yi laifi ba sai an tabbatar da hakan. Sai kaga karamin daki da ya kamata a sa mutane uku ko hudu an cusa mutane 20 a ciki, ba tsafta kuma ba za su yi numfashi mai kyau ba, wannan zai iya kashe mutane, watakila da gangancin za a sa su don su mutu. Wannan za mu ce bai kamata ya faru ba kuma mun yarda da kungiyar Amanesty cewa ya kamata a yi bincike in an samu wanda bai yi aiki yadda ya kamata ba a hukunta shi."

Zargin da Amnesty International ke yi da ta ce mutane da suka mutu mafi yawanci a jihohin Borno da Yobe, musamman a barikin soja na Giwa da ke Maiduguri, inda wasu da aka taba tsaresu suka hakake cewa mutane na mutuwa a kusan kowace rana saboda cunkoso.

An dai dade ana kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin kare hakin jama'a na cikin Najeriya da ma kasa da kasa irin na Amnesty International a kan rufa-rufar da hukumomin Najeriyar ke yi a yaki da masu kai hare-hare a kasar, musamman ma dai jihohi uku da aka kadammar da dokar ta baci.

Logo von Amnesty International, aufgenommen am Donnerstag (12.05.2011) in Berlin bei einer Pressekonferenz. Foto: Britta Pedersen dpa/lbn
Hoto: picture-alliance/dpa

To sai dai ga Malam Dantata Mahmoud na kungiyar kare hakin jama'a da wanzar da zaman lafiya na mai tababa da wannan rahoto.

Shakku ga irin wadannan rahotanni

"To ka san dai kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International ta kasashen Turai ce, kuma irin wadannan kungiyoyi akwai lokutan da suka bada rahotannin da mu da muke cikin Najeriya muka duba cewa ba gaskiya ba ne. To wannan rahoton nasu shin gaskiya ne, in ma haka ne a yanzu dai zargi ne, don haka muna bukatar a bincika."

Hukumomin Najeriyar dai sun ja bakinsu sun yi gum a game da wannan rahoto na kungiyar Amnesty wanda na cikin karin matsin lamba da ake yi wa gwamnati na ta kamanta adalci a yakin da take yi da 'ya'yan wannan kungiya. A lokutan baya dai gwamnatin Najeriyar kan yi biris a kan irin wannan rahoton kafin a karshe ta musanta shi.