1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin sababbin ministoci a Najeriya

LateefaJanuary 22, 2014

Jerin mutane 12 da shugaba Goodluck Jonathan ke neman majalisar dattawa ta tattanace domin nada su ministoci ya nuna a fili yana kokarin nemo bakin zaren yanayin siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/1AvVG
Goodluck Jonathan
Hoto: picture alliance / dpa

To ya dai zabo sababbi da tsofaffi ya chakuda da nufin za su iya zama jarumai da za su jagoranci yunkurin da yake na ci gaba da zama a kan karagar mulkin Najeriyar a zaben 2015. Jerin sunayen mutanen goma sha biyu da ke jiran tantancewar majalisar dattawan kasar da suka hada da tsofaffin da suka ga jiya kuma suke ganin yau irin su Janar Aliyu Gusau da Ambasada Aminu Wali da Mohd Wakil ana masu kallon jarumai a fagen siyasar Najeriyar, musamman a yankin arewacin kasar da farin jinin shugaba Jonathan din ya fadi kasa warwas. Sanya mutanen da suka fuskanci zargin cin hanci da rashawa irin su Boni Haruna daga jihar Adamawa ya sanya jefa alamar tambaya, abin da ya sa Barista Mainasara Ibarahim masani a fagen siyasar Najeriyar tababar samun faruwar hakan.

"Nauyin jagorancin gwamnati lamari ne da ke kan shugaban kasa kuma an bashi izinin ya nada wakilci to in ka dauko mutanen da basu can-canta ba ko baragurbi ka nadasu a kan mukami nauyin a kan shugaban kasa zai koma, musamman a wannan lokaci da shuga Jonathan ke da kalubale na jama'a suma yi na'am da abinda yake yi saboda farin jininsa na ci gaba da raguwa sosai, don haka abu ne kawai na sauya riga sai 'ya'yan wannan ko sai 'yan jamiyyata ko sai wadanda suka iya, to ba za ya kaimu ko ina ba a kasar nan. Kuma wannan abin da ke damunmu kenan, mutum ya rike mukami ya sake rikewa ya yi da tsararrakinsa ya yi da ‘ya'yansa har ya kai ga yanzu yana yi da jikokinsa".

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Sababbin kamu a cikin ministoci dai ana masu kalon sababbin shiga wadanda ke neman dan jagora muddin ana son su yi wani tasiri a cikin harkar musamman a wuraren da suka fito da ko dai 'yan adawa sun yi masu karfi ko kuma suna karkashin wasu iyayen gidansu ne, abinda ba'a hangen wani tasirin da zasu iya yi a wannan gagarumin aiki da ke bukatar jan gwarzo.

Bayanai na nuna cewa tuni aka fara tada jijiyar wuya a tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da ta dage lallai a mayar mata da wakilcinta a sababbin ministocin wanda aka mikawa jihar Kano. To sai dai ga Dr Sadeeq Abba masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja na mai ra'ayin cewa duk lamari ne na yaudara kawai.

ECOWAS Hauptsitz Abuja
Hoto: picture-alliance/dpa

Tsoron makomar da zaben tumun dare ka iya yi ba ga shugaba Jonathan din ba kadai ga ma al'ummar Najeriyar da kan zuba ido cike da fatan majalisar dattawa za ta iya taka birki a wasu al'ammura, abinda ya jefa fata a zukatansu, to amma ga Mainasara Ibrahim na ganin bafa za ta canza zani ba.

A yanzu dai ana jiran ganin mutanen da za'a sauke a majalisar ministocin shugaban na Najeriya da za'a maye gurbinsu da sababbin ministocin, wadanda ya yiwu ko za su iya sauya yadda rawar ke kadawa ga siyasar da shugaban ya samu kansa a ciki mai sarkakiyar gaske.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu/ LMJ