1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kafa kwamitin gano 'yan matan Dapchi

Ramatu Garba Baba
February 28, 2018

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kafa kwamiti na musanman don gudanar da bincike kan sace 'yan matan sakandaren Dapchi da ke a jahar Yobe, acewar ministan yada labaran kasar Lai Mohammed.

https://p.dw.com/p/2tR45
Nigeria Angriff auf Mädchenschule in Dapchi
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ministan yada labaran kasar ya yi karin bayani kan kwamitin wanda zai kasance karkashin jagorancin wani manjo janar, zai gudanar da aikin binciken sanin yadda aka sace 'yan matan ya zuwa samar da shawarwarin don gano inda suke. A makon da ya gabata ne aka sace ‘yan matan dari da goma, masu shekaru tsakanin goma sha daya zuwa sha tara, an kuma zargi mayakan kungiyar Boko Haram da sace su daga makarantan kwanan da ke a Dapchi.

Batun sace 'yan matan ya ja hankalin duniya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bakin kakakinta Stephane Dujarric, ya nemi mahukuntan Najeriya da su gaggauta 'yanto daliban da kuma hukunta wadanda ke da hannun a sace su.