1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bada 'yanci ga majalisu da bangaren shari'a

June 25, 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin hadin gwiwar tabbatar da 'yancin 'yan majalisu da kananan hukumomi da bangaren shari'a.

https://p.dw.com/p/3L4qD
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A wani abu da ke zaman kama hanyar kai wa ga tabbatar da cin gashin kan majalisun dokoki na jihohi da kuma bangaren shari’arsu,  da ranar yau shugaban kasar ya karbi rahoton wani kwamitin hadin gwiwar bangarori na kasar da ke aikin tabbatar da 'yancin mai tasiri. A wasu jihohin kasar irinsu Kogi dai har an kai ga fito na fito a tsakanin gwamantin jihar da bangaren shari’ar, abun kuma da yai sanadin gwamnan tsige babban alkali na jihar,

A yayin kuma da a kusan daukacin jihohi na kasar majalisun dokoki suka sauya daga 'yan doka suka koma yaran gwamnonin da ke iya basu izinin yin doka a cikin tsawon kasa da awoyi 24 ba tare da cika ka’idojin yin dokar ba. Kuma a tsakiyar rikicin dai na zaman batun kudi da ke hannun gwamnoni da kuma suke sarrafa su bisa yadda suke so domin cika burin son rai.

Abun kuma da ke neman sauyawa tare da wani yunkuri a gwamnatin tarrayar Najeriyar na kai karshen babakeren gwamnonin a cikin harkokin majalisun dokoki dana shari’ar. Sashe na 121 na kundin tsarin mulki na kasar dai ya tanadi 'yanci na cin gashin kan ga bangarorin na jihohi guda biyu, kafin sa kafa a take 'yancin a bangaren zartarwar na jihohi mai karfi.

Ana dai kallon 'yancin na kudi a ragowar bangarorin guda biyu na iya kai wa ga karin karfi a demokaradiya ta jihohin da kila tallafawa ya zuwa inganta na tattali na arziki da zamantakewar al’umma na jihohin. Hakazalika ana kallon  sabo na matakin daya biyo bayan 'yanci ga kananan hukumomin na iya kai wa ga rage karfin gwamnonin na jihohin da a baya ake yi wa kallon mamallakan kowane tsari a cikinsu.