1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar yin sulhu da 'yan Shi'a a Najeriya

July 31, 2019

Tun bayan da rundunar 'yan sandar Najeriya ta fara yunkurin kama 'yan Shi'a, masu fafatukar neman lafiya ke nuna bukatar samun maslaha don kaucewa yin fito na fito.

https://p.dw.com/p/3N6RX
Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

Malaman addinai da kungiyoyin al'umma daga sassa dabam-dabam na arewacin Najeriya na ci gaba da  tofa albarkacin bakinsu game da yunkirin kama Musulmin 'yan Shi'a a fadin Najeriya, lamarin kuma na ci gaba da janyo martani da turjiya daga bangarorin shugabanni da sauran 'yan kasar.

Mallam Ibrahim Kufena shi ne sakataren kungiyar Jama'atul Nasril Islam ta jihar Kaduna da ke bayyana cewa ya kamata jami'an tsaro su sani da cewa akwai 'yan Shi'a a kowanne bangaren tsaro da sauran harkokin yau da kullun a cikin kasar.

"Ban sani ba ko sun dauki yawan kidayar 'yan Shi'a da ke a fadin kasar, domin abin da ya kamata a sani shi ne masu fitowa suna zanga-zanga ba dukansu ne 'yan Shi'a ba."

Ya kara da cewa akwai su cikin sojoji da 'yan sanda da sauran bangaren jami'an tsaro da kuma gwamnati.

Akwai 'yan Shi'a cikin rundunonin tsaron Najeriya da sauran hukumomi na gwamnati
Akwai 'yan Shi'a cikin rundunonin tsaron Najeriya da sauran hukumomi na gwamnatiHoto: picture-alliance/AP Photo

Sakataren na kungiyar ta Jama'atul Nasril Islam a Kaduna ya ce abin da ya kamata shi ne gwamnati ta bullo da wata hanyar tattaunawa da su domin kawo karshen fito na fito da sauran tashe-tashen hankula da ke wakana a cikin jihohin arewacin Nigeria, "duk wani yunkurin kama su, babu wani abin da zai haifar face kara tayar da zaune tsaye da kara jefa kasar cikin rudani da zaman dardar."

Fargabar makomar daukar wannan mataki ta sanya sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya C.A.N  a jihar Kaduna yin kira a kan zama kan teburin sulhu da tattaunawa tsakanin Kungiyar IMN ta 'yan Shi'a da gwamnati maimakon matakin na zakulo 'yan Shi'a ana kama su, inji Rev. Dr. Sunday Ibrahim sakataren kungiyar ta C.A.N. a Kaduna

"Ni ina ganin cewa wani babban tashin hankali ne ke tafe a cikin wannan kasar wanda ya fi na kungiyar Boko Haram. Idan da gwamnati ta bi umurnin kotu na sako El-Zakzaky tun da farko, da an magance wannan matsalar da ke kara jefa kasar cikin wani yanayi."

Shi kuwa Sheikh Abdulhamid Bello daya daga manyan malaman Shi'a a Najeriya cewa ya yi akwai bukatar sako jagoransu don samun kwanciyar hankalin daukacin almajiransa.