1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da makwabtanta za su yaki Boko Haram

May 17, 2014

Faransa da Britaniya da kasashe biyar na yammacin Afrika ne dai, suka cimma wannan matsaya a taron da ya gudana a birnin Paris kan rikicin na Najeriya.

https://p.dw.com/p/1C1pN
Frankreich Paris Boko Haram Gipfel 17.5.2014
Hoto: Alain Jocard/AFP/Getty Images

Najeriya da kasashen da ke hada kan Iyaka da ita sun tabbatar da cewar a shirye suke na kaddamar da yaki a kan kungiyar nan ta Boko Haram. A yayin da Britaniya zata taimaka wa sojin Najeriyar da shawarwari kan yadda za su kalubalanci matsalar 'yan kungiyar wadanda yanzu ke zama babbar barazana ga yankin yammacin Afrika baki daya.

A taron da suka gudanar a birnin Paris shugaba Goodluck Jonathan da takwarorinsa na Benin da Chadi da Kamerun tare da Nijar, sun amince da wani tsarin aiki domin yakar kungiyar ta Boko Haram, wadda hare harenta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 2,000 a wannan shekara kadai. Kungiyar dai na fuskatar fushin duniya dangane da sace yara mata sama da 200 daga makarantar sakandare da ke garin Chibok.

Mai masaukin bakin taron kuma shugaban Faransa Francois Hollande, ya jaddada cewar ko shakka babu 'yan kungiyar ta Boko Haram suna da alaka da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda da ke nahiyar Afrika kamar al-Qaeda, wanda ya sanya matsalar kasancewa gagaruma a ilahirin nahiyar baki daya.

Ya ce " ya zamanto dole a dauki mataki da za su kunshi musayar bayanai na da yin martani na gaggauwa idan an samu barkewan kowane irin rikici, da aiki tare tsakanin sojojin kasashen tare da tsaurara matakan tsaro kan iyakoki da kuma tafkin Chadi".

Nigeria Goodluck Jonathan, Boni Yayi & Francois Hollande
Hoto: picture-alliance/dpa

Da yake magana dangane da matsayin Najeriya a kan wannan rikicin na Boko Haram, ministan harkokin wajen Britaniya Willian Hague, cewa ya yi sojojin Najeriya basu da isasshen shiri na tunkarar wannan kungiya. Ana iya ganin hakan ne a cewarsa daga yadda kullum matsaloli sai dada ta'azzara suke. Dalili kenan da Britaniya zata kaiwa kasar dauki a wannan bangaren. Sai dai Hague ya jaddada bukatar gwamnatin Najeriyar ta nuna halin sanin ya kamata wajen sauke nauyi da ya rataya a wuyanta..

Ya ce" Hakki ya rataya a wuyan Najeriya a kan wannan batu, kuma ya zamanto wajibi ta kasance a sawun gaba wajen warware matsalar. Dole ta dauki matakan da suka dace na yin martani idan abu ya faru na samar da tsaro cikin gaggawa, tare da tabbatar da inganta ci gaba da bunkasa tattalin artzikin yankin arewacin kasar. Dukkan wadannan abubuwa ne da ke da muhimmanci".

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce Boko Haram ba kungiyar nan ce data fara fafutukar addini daga shekara ta 2002-2004 ba.

"Tun daga 2009 zuwa yanzu ta rikide irin fafutukarta zuwa salon na kungiyar al Qaeda, don haka ne ya kamata a kirata da sunan al Qaedar yammacin da tsakiyar Afrika. Ta sauya daga manufofinta dake adawa da ilimin boko da tura yara mata karatun boko".

Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan in Brüssels
Hoto: picture-alliance/dpa

Kazalika Goodluck Jonathan ya yi watsi da sukan da ake wa gwamnatinsa na yin tafiyar hawainiya wajen martani kan rikicin na Boko Haram da cewar, a shekara ta 2009 ne Najeriya ta tsinci kanta a wannan riki, kuma kasar bata da ingantacciyyar fasahar kalubalantar lamarin. Ya ce a kawan a tashi sojin Najeriyar za su cimma shawo kan matsalar.

Shima da yake tofa albarkacin bakinsa kan rikicin, shugaba Paul Biya na Kamaru, cewa ya yi Boko Haran ba matsalar Najeriya bace ita kadai, matsalace ta yankin da ma duniya baki daya.

" Mun dauki matakai da suka hadar da sojojin kasancewa cikin shirin kota kwana, zai kasance abu mawuyaci 'yan Boko Haram su kai hari Kamaru, musamman dayake muna tuntubar juna da shugaba Jonathan da sauran wadanda kenan".

Wata majiyar diplomasiyya na kasashen yammaci a wurin taron dai tace, Najeriya ta amince da mikawa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kungiyar ta Boko Haram, domin kakaba mata takunkumi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Salissou Boukari