1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta mayar da martani ga Amirka

Uwais Abubakar Idris LMJ
November 1, 2020

Gwamnatin Najeriya ta bayanna cewa za ta ci gaba da daukar matakan tuntubar masu ruwa da tsaki a zaben 'yar takarar neman shugabancin kungiyar Kasuwanci ta Duniya, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala.

https://p.dw.com/p/3ketF
Kombobild | Ngozi Okonjo-Iweala und Yoo Myung-hee
Ngozi Oknojo-Iweala daga Najeriya tare da Yoo Myung-hee daga Koriya ta Kudu

Wannan matakin dai na zaman martani daga gwamnati dangane da matsayin da Amirka ta dauka a kan kin goyon bayan 'yar takarar ta Najeriya, duk da gagarumin rinjayen da ta samu. Shi ne dai bayani na farko da ya fito daga bangaren gwamnatin Najeriyar, tun bayan da Amirkan karara a fili ta yaye kallabi na kawaici ko wata kunya a kan takarar da 'yar Najeriyar Dakta Ngozi Oknojo-Iweala ke yi na neman zama shugabar kungiyar Kasuwanci ta Duniyar.

Karin Bayani: WTO: 'Yan Afirka uku na neman shugabanci

A sanarwar da ma'aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriyar ta fitar, ta bayyana matakin da za ta dauka a kan batun. Mr  Ferdinand Nwoye shi ne kakakin ma'aikatar, ya kuma yi karin haske: "Kamar yadda muka bayyana a sanarwar da muka fitar, za mu ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a wannan harka domin ba za mu ja da baya ba har sai mun tabbatar da samun nasarar 'yar takararmu a ranar tara ga watan Nuwamba mai zuwa."
'Yar takarar ta Najeriya Oknojo-Iweala dai ta samu gagarumin rinjaye, amma dole sai an jefa kuri'a a ranar tara ga watan Nuwamba mai zuwa, nan da kwanaki 10 kenan kafin ta kai ga darewa kan wannan mukami. Za dai ta fafata ne da 'yar takarar kasar Koriya ta Kudu Yoo Myung–hee. 'Yar takarar ta Najeriyar dai na da gagarumin rinjaye na magoya baya, a wannan takara da take yi dai, inda bayanai suka nuna cewa tana da goyon baya na kasashen Afrika da Tarayyar Turai da Chaina da Japan da kuma Ostiraliya. Abin da ya sanya 'yan Najeriyar da ke da masaniya kan irin wannan matsayi da za ta taka in har ta samu nasara, suka fara mayar da martani.

BG Kandidaten für WTO-Spitzenjob - Die acht Kandidaten
Ngozi Oknojo-Iweala ta yii zarra cikin 'yan takara takwasHoto: picture-alliance/dpa/KEYSTONE/S. Di Nolfi

Karin Bayani: WTO: Ngozi Okonjo-Iweala za ta zama shugaba

To amma fa sai an samu amincewar daukacin kasashen kungiyar su 164 kafin tabbatar da darewar tata kan wannan mukami, abin da ya sanya fafatawa. Sa rai da cikakken fata na kai wa ga samun nasara muhimmin lamari ne, domin Ngozi Oknojo-Iweala za ta zama mace kuma bakar fata ta farko da za ta kai ga wannan mukami, hakan ya sanya kwararru a fanin diplomasiyya na bayyana bukatar kara kaimi na kamun kafa da lallashi da ma ban baki daga Najeriyar, domin ta kai ga samun nasarar.