1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile masu zanga-zanga a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
November 12, 2020

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen zargin cin zarafin da 'yan sanda ke yi a Najeriya da ta tilasta rusa rundunar 'yan sanda ta SARS, suna koken ana matsa musu lamba.

https://p.dw.com/p/3lCJm
Nigeria Lagos | Proteste gegen Polizeigewalt
Jagororin zanga-zangar EndSARS a Najeriya, sun yi zargin ana musguna musuHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Matasan dai sun yi korafin musguna musun ne, biyo bayan  soke rijistar guda daga cikin kungiyoyinsu ta Enough is Enough da mahukuntan Najeriyar Najeriyar suka yi, kasa da makonni biyu bayan da aka rufe  asusun ajiyar mutanen 20 cikin wadanda suka jagoranci wannan zanga-zanga da ma kai wasu mutum 50 kara kotu a Abuja ne dai, Hukumar Kula da yi wa Kamfanonin da Kungiyoyi Rijista a Najeriyar, ta sanar da soke rijistar kungiyar ta Enough is Enough, bisa abin da hukumomi suka kira da saba ka'idoji.

Karin Bayani: Ana ci gaba da mayar da martani kan jawabin Buhari

Matasan da suka yi zanga-zangar ta lumana da ta rikide rikici na kone-kone da asarar dukiya, sun bayyana cewa yunkuri ne na murkushe su a Najeriyar.

Nigeria Ikeja | End Sars Proteste | Demonstranten
Gwamnatin Najeriya na daukar matakai a kan matasan da suka jagoranci zanga-zangaHoto: Pius Utomi EkpeiAFP/Getty Images

Ta dai kai ga danganta su da ayyuka na ta'adanci, bisa zargin cewa kudin da suka rinka samu a matsayin taimako a asusun ajiyarsu, ka haifar da yiwuwar daukar nauyin ayyukan ta'addancin, da daukar nauyinsu ke zaman babban laifi ne a Najeriyar. To sai dai ga Barrsiter Mainasara Umar masani a harkokin shari'a a Najeriya, ya ce bisa tsarin mulkin kasar kungiyoyi irin wadannan ba sa bukatar wata rijista.

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya yi kiran kai zuciya nesa

A yayin da ake wannan gwagwarmayar da aka yi a kan wannan batu da mafi yawa mata ne suka jagoranceta, tuni suke waiwaye na abubuwan da suke ganin ci gabane a gare su. Gwamnatin Najeriyar dai ta ja bakinta ta yi gum, kan cewa duk wani korafi da masu zanga-zangar ke da shi su nufi kotu, kuma ma mafi yawan batutuwan nasu na a gaban kotu domin rarrabe mai gaskiya.