1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasa aiki saboda coronavirus a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 8, 2020

A Najeriya wani bincike da  hukumar kididdigar jama'a ta gudanar, ya gano cewa an samu karin 'yan kasar da ba su da aikin yi saboda matsalar anobar COVID-19 da ke ci gaba da shafar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3dSSa
Afrika Senegal Coronavirus Pasteur Institute in Dakar
Annobar coronavirus ta ta'azzara rashin aikin yi a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan lamarin ya kara jefa mutane da dama cikin halin zaman kashe wando a kasar, kasancewar dubban mutane da ke da aiki a hannunsu sun wayi gari babu, sakamakon yadda ma'aikatu sun rinka yin fyadan 'ya'yan kadanya ga ma'aikatansu. Binciken da hukumar kula da kididdigar jama'ar ta kasar ta fitar, ya nuna cewa kas0 42 na wadanda aka yi binciken a kansu, sun rasa ayyukansu. A cewar Kwamared Nasiru Kabir na kungiyar kwadago ta ULC a Najeriyar wannan ba abu ne da za su lamunta ba.

Kama daga malaman makarantu da rashin komawa bakin aiki ya sanya tura su hutun dole ya zuwa bankuna da kamfanonin jiragen sama, duka labarin daya ne kan batun korar ma'aikata saboda anobar COVID-19. Hakan dai na nuni da kara tabarbarewar matsalar rashin aikin yi, wanda tun tuni ya karu zuwa kaso 23 cikin 100 a zangon karshen shekarar bara. 

Karikatur: Nigeria Jugend Arbeitslosigkeit

Gwamnatin Najeriyar dai ta dade tana ikirarin yunkurin samar da aiki ga al'ummar kasar, tare da alkawarin raba mutane milyan 100 da talauci. Gwamnatin ta ce za ta dauki ma'aikata 1000 a kowace karamar hukuma, cikin kananan hukumomi guda 774 da kasar ke da su.

Mr Festus Keyamo shi ne ministan kasa a ma'aikatar  kwadago da ingantuwar aiki ta Najeriyar, ya kuma ce: "In ka yi la'akari da dukkanin alkalumma na wadanda aka samarwa aikin yi, zaka ga ba wai ba a samar da aikin ba ne, kawai dai yawan al'umma ne ya zarta na aikin da ake samarwa, wannan kuma matsala ce da aka dade da ita. Shi ya sa muka tsara daukar ma'aikata a wannan tsarin domin rage talauci a kuma bunkasa tattalin arziki."

To sai dai ga shugaban hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa a Najeriyar Hassan Bello in an dauki matakan da suka dace, wannan sashin zai cike gibin rashin aikin yi ga tattalin arzikin kasar. Abin da ya bayyana ya zuwa yanzu dai shi ne halin koma baya da anobar cutar COVID-19 din ke haifarwa ga tattalin arzikin Najeriyar, lamarin da ke jefa karin mutane cikin halin tsaka mai wuya.